Kamfanin BUA Ya Shirya Rage Farashin Siminti A Fadin Kasa Baki Daya Don Al'umma

Kamfanin BUA Ya Shirya Rage Farashin Siminti A Fadin Kasa Baki Daya Don Al'umma

  • Kamfanin siminti na BUA karkashin jagorancin Alhaji Abdussamad Rabiu ya yi alkawarin rage farashin siminti a fadin kasar
  • Rabi'u ya bayyana haka ne yayin babban taron kamfanin karo na bakwai a jiya Alhamis 31 ga watan Agusta a Abuja
  • Ya ce zai samar da wadataccen siminti a kasar don samun damar rage farashin madadin shirin gwamnati na fara shigo da shi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Shugaban kamfanin BUA, Abdussamad Rabiu ya ce sun shirya tsaf don rage farashin siminti a fadin kasar.

Kamfanin ya ce zai yi hakan ne don dafa wa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu wurin inganta tsare-tsarensa na tattalin arziki Legit.ng ta tattaro.

Kamfanin siminti na BUA zai rage farashin siminti a Najeriya
Kamfanin Siminti Na BUA Ya Shirya Rage Farashi A Fadin Najeriya. Hoto: Legit.ng.
Asali: Instagram

Meye BUA ya ce game da siminti?

Attajirin ya bayyana haka ne a jiya Alhamis 31 ga watan Agusta a Abuja yayin babban taron kamfanin karo na bakwai, Daily Trust ta tattaro.

Kara karanta wannan

Matashi Dan Shekara 20 Ya Kashe Mahaifinsa Don Asirin Neman Abin Duniya, Bayanai Sun Fito

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce kamfanin ya himmatu wurin tabbatar da kara samar da siminti a fadin kasar baki daya.

A cewarsa:

"Zuwa karshen wannan shekara mu na fatan kara samar da siminti a kamfanonin mu guda biyu don kara yawan siminti da mu ke fitarwa da kaso 40.
"Hakan zai taimaka wurin samun wadataccen siminti zuwa tan miliyan 70.
"Dalilin kara yawan samar da simintin shi ne don rage farashin madadin shigo da shi kasar wanda hakan ba alkairi ba ne."

Meye BUA ya ce kan shigo da saminti?

Ya kara da cewa a yanzu farashin siminti ya kai Naira 4,500 wanda hakan ke nuna tan daya ya kai Naira 90,000 kenan ko kuma Dala 100.

Idan kuma gwamnati ta ce za ta fara shigo da shi kasar, to hakan zai kara farashin ne ba ragewa ba duba da abubuwan da su ke ciki.

Kara karanta wannan

'Wike Zai Kare a Gidan Yari', Wanda Aka Rusawa Gini Ya Sha Alwashin Shiga Kotu

Wani masanin gine-gine, Architect Muhammad Auwal Akko ya ce tabbas hakan zai taimaka wurin habaka harkokin gine-gine.

Ya ce:

"Hakan zai taimaka wurin saukin yin gine-gine, kasancewar siminti shi ne ginshikin yin duk wani gini.
"Sannan yawan akin gine-gine ya na da tasiri wajen yaduwar arziki a cikin kasa.

Ya kara da cewa:

"Ina kira ga abokan sana'ar BUA a fannin siminti, da suyi koyi da shi wajen saukar da farashin domin samun saukin rayuwa."

Har ila yau, Architect Muhammad Adamu Dokoro ya ce rage farashin zai yi matukar dawo da harkar gine-gine.

Ya ce a yanzu sakamakon tashin farashin, harkokin gine-gine sun ja baya sosai.

A cewarsa:

"Rage farashin abu ne da zai kara farfado da harkar gini, sakamakon tashin farashin abubuwa da dama sun ja baya a harkar gine-gine.
"Mu na farin ciki da wannan saboda abubuwa za su tafi dai-dai yadda ake so, kuma hakan zai kara habaka tattalin arziki."

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Sake Ware Biliyoyin Kudade Don Sake Gina Arewa, Ya Bayyana Dalili

Yayin da Muhammadu Mesin ya ce ya ji dadin haka saboda tsadar simintin na hana su samun ayyuka a lokuta da dama.

Dan Biloniya BUA Yayi Murabus Daga Kasuwancin Mahaifinsa

A wani labarin, 'Dan biloniyan 'dan kasuwa, Rabiu Abdulsamad Rabiu, ya yi murabus daga matsayin zababben daraktan kamfanin BUA Foods Plc.

Naziru ya bar kamfanin mahaifinsa tun daga ranar 17 ga watan Augusta a shekarar 2022 kamar yadda takardar da kamfanin ya fitar ta bayyana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel