Gwamna Ya Waiwaiyi Daliban Jiharsa, Zai Fara ba kowane Dalibi Tallafin N200,000
- Gwamna Umo Eno ya yi alƙawarin ƙara tallafin karatun ɗaliban manyan makarantu daga N50,000 zuwa N200,000 a shekara idan ya sake lashe zaɓen 2027
- Ɗaliban da ke karatun likitanci, lauya da injiniyanci za su riƙa samun N250,000 a kowace m shekara
- Gwamnan ya kuma yi alƙawarin gina ƙarin gidaje 1,000 ga marasa galihu tare da ba su tallafin jari na N500,000 kowannensu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Akwa Ibom, Nigeria - Gwamnan jihar Akwa Ibom, Fasto Umo Eno, ya sanar da shirin ƙara tallafin karatun ɗaliban manyan makarantun gaba da sakandire daga N50,000 zuwa N200,000 a duk shekara.
Gwamnan ya kuma sha alwashin cewa ɗaliban da ke karatun fanonin likitanci, lauya da injiniyanci za su riƙa samun N250,000 a matsayin tallafin karatu a kowace shekara.

Source: Twitter
Tashar Channels ta ruwaito cewa Eno ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa a rana ta biyu ta taron Ibom Ignite na shekarar 2026, wanda aka gudanar a Ibom Hall da ke Uyo ranar Laraba.
Gwamna Eno zai kara tallafin karatu
Ya bayyana cewa za a fara aiwatar da ƙarin tallafin ne idan ya sake lashe zaɓen gwamnan jihar da za a gudanar a watan Fabrairun 2027, sannan ya kama aiki a wa’adi na biyu.
Gwamna Eno ya ce an tsara ƙarin tallafin ne domin taimaka wa ɗalibai wajen biyan kuɗaɗen karatunsu cikin sauƙi.
Ya ƙara da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tabbatar da ilimi kyauta kuma wajibi a matakin firamare da sakandare.
An raba tallafin Naira miliyan 50
Ya kuma shawarci waɗanda suka ci gajiyar tallafin jari na Naira miliyan 50 da shirin Ibom Ignite ya bayar da su yi amfani da kuɗin yadda ya kamata domin bunƙasa kasuwancinsu da inganta rayuwarsu.
Gwamnan ya bayyana tallafin a matsayin jarin farko da aka bayar domin taimaka wa mutane su haɓaka sana’o’insu, yana mai gargaɗin waɗanda suka amfana da su guji kashe kuɗin wajen jin daɗin kansu ko harkokin da ba za su samar musu da riba ba.

Kara karanta wannan
Zance ya ƙare, INEC ta amince da takarar Sheikh Pantami da Aminu Gwarzo a zaɓen 2027
“Ƙwayar shuka da ba a dasa ta yadda ya kamata kuma ba a kula da ita ba, tamkar matacciya ce,” in ji shi, yayin da yake ƙarfafa matasa ’yan kasuwa su yi amfani da kuɗin cikin hikima tare da ƙoƙarin cimma burin kasuwancinsu.

Source: Facebook
Tallafin marasa galihu
Da yake magana kan tallafin da gwamnatinsa ke bai wa marasa galihu, Eno ya ce an gina gidaje sqQama da 500, wato Compassionate Homes, domin taimaka wa marasa galihu a faɗin ƙananan hukumomi 31 na jihar.
Ya ƙara da cewa kowane wanda ya ci gajiyar shirin ya samu tallafin jari na N500,000 domin taimaka masa wajen samun abin dogaro da kai.
Gwamnan ya yi alƙawarin gina ƙarin gidaje1,000 tare da bayar da tallafin jarin da ke tattare da shirin a dukkan mazabun jihar Akwa Ibom idan aka sake zaɓensa a wa’adi na biyu.
Gwamna Eno ya tuna sana'ar kosai
Kun ji cewa gwamnan Akwa Ibom, Umo Eno, ya bayyana cewa ya taba samun kudin shiga Naira miliyan 10 a duk wata daga sana'ar sayar da kosai da burodi.
Gwamnan ya ce ya fara sana'ar ne tun lokacin da yake dan kasuwa, inda ya rika sayar da kosai da burodi ga ma'aikatan kamfanin ExxonMobil.
Asali: Legit.ng
