Hanyoyin da INEC za Ta Bi Ta Magance Tashin Hankali a Zaben 2027

Hanyoyin da INEC za Ta Bi Ta Magance Tashin Hankali a Zaben 2027

  • Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta kaddamar da sabon tsarin tsaro da zai taimaka wajen dakile tashin hankali gabanin babban zaben 2027
  • Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya yi gargadin cewa duk wanda ya yi barazana ga ma’aikatan wucin gadi, masu yi wa kasa hidima ko ma’aikatan hukumar zai fuskanci hukunci
  • Ya bayyana cewa sabon tsarin zai mayar da hankali kan gano wuraren da ke da hadarin rikici tun da wuri, kare masu zabe da jami’an zabe, tare da tabbatar da tsaro a rumfunan zabe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayyana cewa za ta yi amfani da sabon tsarin tsaro da ya dogara da bayanan sirri domin dakile tashin hankali gabanin babban zaben 2027.

Kara karanta wannan

Shugaban INEC ya yi maganar goyon bayan wani ‘dan takara zaben 2027

Shugaban hukumar, Farfesa Joash Amupitan, SAN, ne ya bayyana hakan a ranar Talata a Gombe, yayin bude taron tuntuba da ma’aikatan shiyyar Arewa maso Gabas da kuma tantance shirye-shiryen zaben 2027.

Shugaban INEC, Joash Amupitan
Lokacin da shugaban INEC ya ziyarci IBB a Neja. Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

Vanguard ta wallafa cewa INEC ta ce za ta sauya daga tsarin tura jami’an tsaro a ranar zabe kawai zuwa wani tsari da zai fara kare masu zabe, ma’aikata da kayayyakin zabe tun kafin a kai takardun kada kuri’a rumfuna.

Sabon tsarin tsaron INEC

Amupitan ya ce hukumar ta sake fasalin hadin gwiwarta da rundunar ’yan sanda, hukumar tsaron farin kaya ta NSCDC, hukumar DSS, rundunar sojoji da sauran hukumomin tsaro karkashin kwamitin tuntuba kan tsaron zabe (ICCES).

Ya bayyana cewa sabon tsarin da hukumar ta kira “ICCES T” zai fadada hadin gwiwar hukumomin tsaro daga matakin kasa da jihohi zuwa kananan hukumomi da cibiyoyin rajistar masu zabe, har da wadanda ke yankunan da ke da wahalar isa.

Shugaban INEC ya ce babu yadda za a ce zabe ya kasance sahihi idan masu kada kuri’a, jami’an zabe da masu sa ido suna fuskantar barazanar tashin hankali ko tsoron kai musu hari.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya ba da mamaki, ya dauki alkawari shiga dazuka da afafunsa

Ya bayyana cewa tsarin ya kunshi muhimman ginshikai guda uku, wadanda za su taimaka wajen tabbatar da tsaron zabe tun kafin fara kada kuri’a.

Ginshikai 3 na tsarin

Ginshiki na farko shi ne gano wuraren hadari da daukar matakan rage barazanar tsaro. A karkashinsa, hukumar za ta yi amfani da kayan aikin tantance hadarin zabe domin gano wuraren da ka iya fuskantar rikici, matsalolin yanayi da sauran barazana.

Na biyu shi ne tabbatar da tsaro ga ma’aikatan zabe, na’urorin fasaha da sauran kayayyakin hukumar, ciki har da na’urar tantance masu zabe ta BVAS da na’urorin adana bayanai. Haka kuma, tsarin zai ba da muhimmanci wajen kare masu kada kuri’a.

Ginshiki na uku shi ne tabbatar da cewa dukkan rumfunan zabe 176,846 da ke fadin Najeriya sun kasance wuraren da jama’a za su iya kada kuri’a cikin kwanciyar hankali da mutunci.

Wajen zaben jihar Osun
Jami'an INEC a wajen zaben Osun na 2026. Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

Masu zabe a Arewa maso Gabas

Amupitan ya ce yankin Arewa maso Gabas na da kalubale na musamman wajen gudanar da zabe, saboda akwai manyan yankunan hamada, wuraren da ruwa ya mamaye, kauyuka masu nisa da kuma fadin kasa.

Kara karanta wannan

Matasa sun shiga babbar matsala da suka jefi magoya bayan APC a tawagar gwamna

Sai dai ya yaba da juriyar al’ummar yankin da kuma yadda suke nuna himma wajen shiga harkokin dimokuradiyya.

Ya bayyana cewa yankin na da masu kada kuri’a 13,965,475, wanda ya kai kashi 13.51 cikin 100 na jimillar masu zabe sama da miliyan 103 da ke Najeriya.

Jihar Bauchi ce ke kan gaba da masu zabe 3,012,547, sai Borno mai 2,765,165, Adamawa mai 2,431,146, Taraba mai 2,254,380, Gombe mai 1,768,566 da Yobe mai 1,733,671.

INEC ta ce za ta yi adalci

A baya, mun rahoto cewa shugaban INEC, Joash Amupitan, ya bayyana cewa hukumar ba ta da dan takarar da take so ko wata jam’iyyar siyasa da take goyon baya a babban zaben 2027.

Ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a lokacin da ya karbi bakuncin tawagar kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) a Abuja.

Amupitan ya ce hukumar na gudanar da rangadin tantance shirye-shiryen zabe a shiyyoyi daban-daban na Najeriya, domin tabbatar da cewa an shirya gudanar da zaben 2027 cikin adalci.

Ya kuma bayyana cewa za a gudanar da zaben ne a cibiyoyin rajista 8,809 da kananan hukumomi 774 na kasar, yana mai jaddada cewa INEC za ta yi biyayya ga doka da kuma zabin al’ummar Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng