Masussuka: Tinubu Bai Ji Daɗin Kisan Gillar da Aka Yi wa Sheikh ba, Ya ba da Umarni

Masussuka: Tinubu Bai Ji Daɗin Kisan Gillar da Aka Yi wa Sheikh ba, Ya ba da Umarni

  • Shugaba Bola Tinubu ya yi Allah wadai da kisan fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka, da abokinsa, Adamu Abubakar
  • Tinubu ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan kisan malamin da abokinsa, tare da cafke waɗanda suka aikata laifin domin gurfanar da su
  • Shugaban ƙasa ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan, mabiyansu da al’ummar Katsina, tare da addu’ar Allah Ya jiƙansu, Ya kuma ba masu alhinin mutuwarsu haƙuri

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Shugaban ƙasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya yi Allah wadai da kisan fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka, da abokinsa, Adamu Abubakar, a Dutsin-Ma, Katsina.

Shugaban ƙasar ya kuma bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan musabbabin mutuwar mutanen biyu, inda ya ce dole ne a kamo waɗanda suka aikata laifin, a hukunta su.

Kara karanta wannan

Sheikh Ahmad Gumi ya fitar da saƙo kan kisan da aka yi wa Masussuka a Katsina

Tinubu ya jimamin rashin Sheikh Masussuka
Marigayi Sheikh Ibrahim Yahaya Masussuka. Hoto: Sheikh Ibrahim Yahaya Masussuka.
Source: Facebook

Umarnin Tinubu kan kisan Masussuka

Da yake mayar da martani kan lamarin, Bayo Onanuga, mai ba shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai da dabarun sadarwa, ya ce Tinubu ya kaɗu matuƙa da labarin kisan.

Wasu ’yan bindiga ne suka kashe malamin da abokinsa a wani harin bindiga da suka kai musu a lokacin da suke cikin mota, a yammacin ranar Litinin.

Shugaban ƙasar ya bayyana kisan a matsayin wani mummunan aiki da ke cin zarafin ƙimomin zaman lafiya da tsarkin rayuwar ɗan Adam.

Onanuga ya ce Shugaba Tinubu ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan, mabiyansu, da gwamnatin Katsina da al’ummar jihar baki ɗaya bisa wannan babban rashi da suka yi.

Ya ce shugaban ƙasar ya umarci rundunar ’yan sandan Najeriya da sauran hukumomin tsaro da abin ya shafa da su gaggauta ɗaukar mataki, tare da ƙarfafa binciken da rundunar ’yan sandan Katsina ta fara.

Ya ƙara da cewa Tinubu ya umurci jami’an tsaro da su gano waɗanda suka aikata kisan, su cafke su, sannan a gurfanar da su domin fuskantar hukunci bisa doka.

Kara karanta wannan

Farfesa Makari ya yi magana kan kashe Sheikh Masussuka

Shugaba Tinubu ya yi addu’ar Allah Ya jiƙan waɗanda aka kashe, Ya gafarta musu, sannan Ya ba iyalansu da duk waɗanda suke jimamin rasuwarsu haƙurin jure wannan babban rashi.

Ƙarin bayani na tafe.....

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.