Damuna na Nan: NiMet Ta Fadi Jihohin da za a Yi Ruwan Sama

Damuna na Nan: NiMet Ta Fadi Jihohin da za a Yi Ruwan Sama

  • Hukumar NiMet ta yi hasashen samun ska da guguwa mai dauke da ruwan sama a sassa daban-daban na Najeriya daga Juma’a zuwa Lahadi
  • Hukumar ta ce wasu jihohin Arewa za su fuskanci hazo, yayin da ake sa ran ruwan sama a jihohin Arewa ta Tsakiya da Kudancin ƙasar
  • NiMet ta shawarci masu fama da asma da sauran cututtukan numfashi su yi taka-tsantsan, tare da gargadin jama’a kan illar iska mai ƙarfi da tsawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi hasashen samun ƙurar iska da ruwan sama a sassa daban-daban na ƙasar daga ranar Juma’a zuwa Lahadi.

Kara karanta wannan

Obi ya fadi yadda zai yi aiki tare da Kwankwaso idan suka yi nasara a 2027

Hasashen yanayin, wanda hukumar ta fitar a ranar Alhamis a Abuja, ya nuna cewa wasu yankunan Arewa za su fuskanci hazo, yayin da ake sa ran samun ruwan sama a yankunan Arewa ta Tsakiya da Kudancin Najeriya.

Ana ruwan sama a Gombe
Yara na wasa a ruwan sama a Nafada, Gombe. Hoto: Abba Abubakar
Source: Facebook

Jihohin da za a yi ruwa/hazo

Punch ta rahoto NiMet ta bayyana cewa za a samu hazo da iska a mafi yawan yankunan Arewa, yayin da ake sa ran ƙurar za ta fi yawa a wasu sassan jihohin Kano, Jigawa, Bauchi da Kaduna.

Hukumar ta kuma yi hasashen samun ruwan sama mai sauƙi tare da tsawa a wasu sassan jihar Taraba da yammacin Juma’a.

A yankin Arewa ta Tsakiya kuwa, za a samu rana tare da ɗan gajimare. Ana kuma sa ran ruwan sama mai sauƙi da tsawa a wasu sassan jihohin Kogi, Kwara, Benue da Babban Birnin Tarayya, Abuja.

A Kudancin ƙasar, hukumar ta ce za a samu gajimare, tare da yiwuwar ɗan ruwan sama a wasu sassan jihohin Delta da Bayelsa da safiyar Juma’a.

Kara karanta wannan

Najeriya ta nuna damuwa kan 'yan kasar ta da ke Faransa ana zanga zanga

Daga baya, ana sa ran samun ruwan sama mai matsakaicin ƙarfi tare da tsawa a wasu sassan jihohin Ondo, Ogun, Osun da Ekiti, da kuma yankunan Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu.

Hasashen yanayin ranar Asabar

Hukumar NiMet ta ce za a samu rana dauke da hazo a dukkan yankunan Arewa a ranar Asabar mai zuwa.

A yankin Arewa ta Tsakiya kuwa, ana sa ran samun rana tare da ɗan gajimare da safe, yayin da daga baya ake hasashen ruwan sama mai sauƙi tare da tsawa a wasu sassan jihohin Kogi, Kwara da Benue.

A Kudancin Najeriya, za a samu gajimare da safe, sannan a samu ruwan sama mai matsakaicin ƙarfi tare da tsawa a mafi yawan yankunan da rana.

Yadda ake hazo a Najeriya
Mutane na tafiya a cikin hazo. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Hukumar ta shawarci jama’a da su ɗauki matakan kariya daga ƙurar da ke shawagi a iska, musamman mutanen da ke fama da asma da sauran cututtukan da suka shafi numfashi.

Za a inganta noma a Najeriya

A wani labarin, kun ji cewa Kashim Shettima ya bayyana cewa Najeriya za ta yi amfani da tsarin bunƙasa aikin noma na yankin Oromia da ke ƙasar Habasha domin tabbatar da wadatar abinci.

Kara karanta wannan

Rana ba ta karya: Yau INEC za ta yi matsaya kan Pantami da wasu 'yan takara

Shettima ya yi gargaɗin cewa ƙasar da ta dogara da wasu ƙasashe wajen ciyar da al'ummarta na fuskantar barazana ga 'yancinta da ikonta na ƙasa a nan gaba.

A wani mataki na koyi da tsarin kiyaye muhalli na Habasha, Najeriya ta tsara ƙaddamar da shirin dasa bishiyoyi biliyan 20 a lokacin damina mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng