Najeriya Ta Nuna Damuwa kan 'Yan Kasar Ta da ke Faransa Ana Zanga Zanga

Najeriya Ta Nuna Damuwa kan 'Yan Kasar Ta da ke Faransa Ana Zanga Zanga

  • Hukumar NiDCOM ta bukaci ’yan Najeriya da ke zaune a Faransa su kwantar da hankula tare da guje wa tashin hankali yayin da ake gudanar da zanga-zanga a ƙasar
  • Shugabar hukumar, Abike Dabiri-Erewa, ta shawarci ’yan Najeriya su guji faɗa, yada jita-jita da bayanan da ba a tabbatar da sahihancinsu ba a kafafen sada zumunta
  • Hukumar ta kuma bukaci ’yan Najeriya da ke Faransa su mutunta dokokin ƙasar, su bi umarnin jami’an tsaro, tare da neman taimakon ofishin jakadanci ko hukumomin gaggawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Hukumar kula da ’yan Najeriya mazauna ƙasashen waje (NiDCOM) ta yi kira ga ’yan Najeriya da ke zaune a Faransa da su kwantar da hankula, su kiyaye zaman lafiya tare da mutunta dokokin ƙasar da suke zaune a ciki.

Kara karanta wannan

Rana ba ta karya: Yau INEC za ta yi matsaya kan Pantami da wasu 'yan takara

Shugabar hukumar kuma babbar jami’arta, Abike Dabiri-Erewa, ce ta yi kiran a cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na hukumar, Abdur-Rahman Balogun, ya fitar a ranar Alhamis.

Shugaba Bola Tinubu da Emmanuel Macron
Shugaban Faransa tare da Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

A sakon a hukumar ta wallafa a X, ta bukaci ’yan Najeriya su guji duk wani abu da zai iya haddasa rikici, tare da yin aiki da umarnin hukumomin Faransa na halal.

NiDCOM ta gargadi ’yan Najeriya

Dabiri-Erewa ta shawarci ’yan Najeriya da ke Faransa da su guji faɗa, tashin hankali da tsokana, tare da nuna halin dattako a duk inda suke.

Ta ce ya kamata su kiyaye zaman lafiya da bin doka, musamman a wannan lokacin da zanga-zanga ke gudana a sassa daban-daban na Faransa.

Shugabar hukumar ta kuma bukaci ’yan Najeriya su mutunta maƙwabtansu da sauran al’ummomi ba tare da la’akari da ƙasa, addini ko asalin mutum ba.

A cewarta, ’yan Najeriya da ke zaune a ƙasashen waje suna wakiltar ƙasarsu, don haka suna da alhakin kiyaye mutuncin Najeriya yayin da suke mutunta dokokin ƙasashen da suke zaune.

Hukumar ta gargadi jama’a kan yada jita-jita

Kara karanta wannan

Sojoji sun ceto mutane 70, sun kama ƙasurgumin ɗan bindiga da ya addabi mutane a Arewa

Hukumar NiDCOM ta kuma bukaci ’yan Najeriya da su riƙa dogaro da sahihan bayanai kan tsaro, maimakon yaɗa jita-jita ko labaran da ba a tabbatar da su ba, musamman a kafafen sada zumunta.

Yadda ake zanga-zanga a Faransa
Masu zanga-zanga a Faransa. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Dabiri-Erewa ta shawarci duk wanda yake ganin tsaronsa ko haƙƙoƙinsa na cikin barazana da ya nemi taimakon doka, tare da tuntuɓar hukumomin gaggawa ko ofishin jakadancin Najeriya da ya dace.

Ta kuma yi kira ga shugabannin al’ummar Najeriya a Faransa, iyalai, ɗalibai, ƙwararru da ƙungiyoyin al’umma da su haɗa kai wajen inganta zaman lafiya da haɗin kai.

Hukumar ta jaddada cewa ya kamata ’yan Najeriya su guji tashin hankali, su bi shawarwarin tsaro da aka tabbatar, tare da bin umarnin hukumomin Faransa na halal.

Shugaban Faransa ya fasa zuwa Najeriya

A wani labarin, mun ruwaito cewa Faransa na ƙoƙarin farfaɗo da dangantakarta ta tarihi da ƙasashen Afirka ta Yamma bayan ta samu matsala a hulɗarta da ƙasashen da ke cikin Ƙungiyar Ƙasashen Sahel (AES).

A wani ɓangare na ƙoƙarin ƙarfafa hulɗar diflomasiyya da tattalin arziki, an shirya ziyarar shugaban Faransa Emmanuel Macron zuwa Najeriya da Senegal a watan Oktoba na 2026.

Sai dai an soke ziyarar yayin da zanga-zanga da tashe-tashen hankula suka ƙaru a cikin Faransa, kuma ba a bayyana sabon lokacin da za a gudanar da ita ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng