'Yan bindiga sun yi awon gaba da matar aure da ɗan ta a Katsina

'Yan bindiga sun yi awon gaba da matar aure da ɗan ta a Katsina

- Ƴan bindiga sun bi wata matar aure har gidan mijinta tsakar dare sun yi awon gaba da ita a Katsina

- Ƴan bindigan sun afka gidan sa a daren ranar Talata inda suka yi awon gaba da matar da ɗan sa

- Kakakin 'yan sandan jihar Katsina ya tabbatar da afkuwar lamarin amma ta ce tana jiran cikakken bayani daga DPO na yankin

'Yan bindiga sun yi awon gaba da matar aure da ɗan ta a Katsina
Taswirar jihar Katsina. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

'Yan bindiga sun sace matar wani Alhaji Mai Yadi Charanci da ɗan sa mai shekaru 3 a ƙaramar hukumar Charanci ta jihar Katsina.

Mazauna garin sun ce lamarin ya faru ne misalin ƙarfe 12.30 na daren ranar Talata.

An ruwaito cewa yan bindigan sun afka gidan mutumin da ke unguwar Gabas a Charanci suka sace su.

DUBA WANNAN: Gwamnan jihar Gombe ya nada dan kabilar Igbo a matsayin hadiminsa (Hotuna)

Ba a tabbatar ko mutanen dauke da makaman ƴan bindiga ne ko kuma bata gari ba da ke garkuwa don neman kudin fansa.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, SP Gambo Isah ya tabbatar da afkuwar lamarin.

Ya kara da cewa suna jiran karin bayani daga DPO na yan sandan yankin.

"Abin ya faru da gaske, amma dai muna jiran karin bayani daga DPO na yankin," in ji Isah.

KU KARANTA: Zaben kananan hukumomi: Gwamnatin Kano za ta yi wa 'yan takara gwajin kwayoyi

A halin yanzu wadanda suka sace su ba su tuntuɓi iyalan su ba a lokacin rubuta wannan rahoton.

Gwamnatin jihar a ranar Talata ta shirya taron wayar da kai kan tsaro ga shugabannin ƙananan hukumomi da hakimai.

A wani labarin, Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno a ranar Talata ya amince a ɗauki sabbin malamai 776 don inganta ilimi a makarantun gwamnatin jihar.

Gwamnan ya sanar da hakan ne jim kadan bayan gana wa da ya yi da jami'an Ma'aikatar Ilimi na jihar a gidan gwamanti da ke Maiduguri.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel