Cikin Mata Mai Juna Biyu da 'Yan Bindiga Suka Sace Ya Zube a Daji

Cikin Mata Mai Juna Biyu da 'Yan Bindiga Suka Sace Ya Zube a Daji

  • Wata mata mai juna biyu mai suna Jamila, wadda ’yan bindiga suka sace a Millennium City da ke Kaduna, ta shafe mako uku a hannun masu garkuwa da mutane
  • Wata majiya ta ce Jamila ta sanar da iyalanta cewa ta zubar da cikin da take ɗauke da shi, yayin da masu shiga tsakani ke ci gaba da ƙoƙarin ganin an kuɓutar da ita
  • Satar mutane na ci gaba da addabar Millennium City, inda wasu iyalai ke zaman jiran dawowar ’yan uwansu da aka sace a hare-hare daban-daban

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna – Wata mata mai juna biyu mai suna Jamila, wadda ’yan bindiga suka sace daga gidanta a Alrahus Estate da ke Millennium City, jihar Kaduna, har yanzu tana hannun masu garkuwa da mutane mako uku bayan sace ta.

Kara karanta wannan

An farmaki yan APC yayin da Gwamna Radda ya kaddamar da kamfen a Katsina

An sace Jamila ne a ranar 6 ga Oktoba, tare da Abubakar Zakka, matarsa da jaririyarsu mai watanni shida, lokacin da ’yan bindigar suka kai hari gidansu da ke ƙaramar hukumar Chikun.

Taswirar jihar Kaduna
Taswirar jihar Kaduna. Hoto: Legit
Source: Original

Cikin Jamila ya zube a daji

Wata majiya da ke da masaniya kan tattaunawar da ake yi domin kuɓutar da Jamila ta bayyana wa Daily Trust cewa masu garkuwar sun kira a ranar Talata, inda suka ba ta wayar domin ta yi magana da iyalanta.

A cewar majiyar, Jamila ta sanar da su cikin kuka cewa ta zubar da cikin da take ɗauke da shi bayan sace ta da aka yi.

Majiyar ta ce lamarin ya jefa su cikin baƙin ciki, amma suna ci gaba da ƙoƙarin ganin an kuɓutar da ita daga hannun masu garkuwar.

Har zuwa lokacin da aka tattara rahoton, ba a samu cikakken bayani kan halin da Jamila take ciki ko lokacin da za a iya kuɓutar da ita ba.

An saki Zakka da matarsa

Abubakar Zakka, matarsa da jaririyarsu mai wata shida sun samu ’yanci kwanaki kaɗan bayan sace su.

An ruwaito cewa sakin nasu ya biyo bayan yaɗuwar wani bidiyo a kafafen sada zumunta, wanda ya nuna wani ɗan bindiga yana nufar kan ɗaya daga cikin waɗanda aka sace da bindiga, yayin da jaririyar ke kuka.

Kara karanta wannan

Matatar Dangote ta kafa tarihi bayan kammala sayar da hannayen jari

Sai dai wasu mazauna Millennium City da aka sace a hare-hare daban-daban har yanzu suna hannun masu garkuwa da mutane.

Gwamna Uba Sani
Gwamnan jihar Kaduna a ofis. Hoto: Kaduna State Government
Source: Facebook

Wani ɗan uwa ga mutumin da ’yan bindiga suka kashe a yankin Babban Saura PW ya ce har yanzu suna addu’ar Allah Ya dawo musu da matarsa da ɗansa da aka sace.

Ya bayyana cewa sun dogara da addu’a ne domin neman taimakon Allah, yana mai cewa raɗaɗin da iyalan ke ciki abu ne mai tsanani da ba zai yi wa ko maƙiyinsa fatan fuskanta ba.

Bafarawa ya magantu kan tsaro

A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa, ya bayyana cewa zai yi wa Shugaba Bola Tinubu kamfen idan gwamnatinsa ta magance matsalar tsaro.

Bafarawa, wanda ya mulki jihar Sokoto daga 1999 zuwa 2007, ya bayyana hakan ne a wata hira, inda ya ce zai goyi bayan Tinubu ne idan an dawo da zaman lafiya.

Tsohon gwamnan ya ce har yanzu Tinubu yana da damar magance matsalar tsaro kafin zaɓen, yana mai cewa idan aka samu zaman lafiya, zai goyi bayan yaƙin neman zaɓensa kuma ya zaɓe shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng