Yanzu-yanzu: An hari jirgi bayan saukarsa a filin jirgin Murtala Mohammed da ke Legas

Yanzu-yanzu: An hari jirgi bayan saukarsa a filin jirgin Murtala Mohammed da ke Legas

- Wasu mahara da ba a ganosu ba har yanzu sun hari jirgin sama a filin sauka da tashin jiragen sama na Murtala Muhammed dake Legas

- An zargi cewa maharan sun bude wajen ajiye kayan matafiya ne bayan saukar jirgin

- Idan zamu tuna, ba wannan ne karo na farko ba da aka fara samun karantsaye ga lamarin tsaro a filin jirgin

Wasu mahara da ba a gano su ba har yanzu sun hari jirgin saman kasar Morocco yayin sauka a filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Legas.

An zargi cewa, maharan sun bude bangaren ajiye kayan matafiya ne na jirgin.

An hari jirgin ne a hanyar sauka da tashin jirage na filin sauka da tashin jiragen sama na Murtala Muhammed da ke Legas a safiyar juma'a.

KU KARANTA: Majalisar jihar Legas ta yi barazanar kama tsohon gwamnan jihar

Majiyar kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, ta ce an hari jirgin ne bayan ya sauka a filin jirgin a sa'o'in farko na ranar Juma'a.

Jirgin ya taso ne daga Rabat inda ya sauka a Legas inda abin ya faru.

Filin sauka da tashin jiragen saman na Murtala Muhammed din na daga cikin filayen jirage mafi hada-hada a Najeriya. Ya samu matsalalolin tsaro ba karo na farko ba kenan a tarihi.

Idan zamu tuna, a ranar 21 ga watan Yuli, wani mai matsalar kwakwalwa ya shiga filin jirgin inda ya hau fiffiken jirgin da ke kokarin tashi.

Bayan aukuwar lamarin, hukumar kula da filayen jiragen saman Najeriya ta dakatar da manajan filin jirgin da manyan jami'an tsaro akan karantsaye da aka yi wa tsaron wajen.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel