An Bayyana Irin Manyan Makaman da Najeriya za Ta Fara Kerawa

An Bayyana Irin Manyan Makaman da Najeriya za Ta Fara Kerawa

  • Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa mai ritaya, ya ce Najeriya za ta fara samar da kayan aikin tsaro da makaman soji da yawa a cikin gida a shekara mai zuwa
  • Ya bayyana cewa za a samar da kayan aikin domin amfanin Najeriya da kuma fitar da su zuwa wasu ƙasashen duniya, musamman na Afirka
  • Ministan ya yi kira ga masu zuba jari da sauran masu ruwa da tsaki da su yi amfani da baje kolin AFRIDEX wajen saka hannun jari a ɓangaren tsaron Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Legas Lagos – Ministan Tsaro na Najeriya, Janar Christopher Musa mai ritaya, ya bayyana cewa ƙasar za ta fara samar da kayan aikin tsaro da makaman soji a cikin gida da yawa a shekara mai zuwa.

Kara karanta wannan

Ziyarar Hannatu Musawa ofishin uban ‘ya ‘yanta, Abdussamad ya dawo da batun aure

Ya bayyana cewa za a fara hada makaman ne domin biyan buƙatun ƙasar da kuma fitar da su zuwa wasu ƙasashe, musamman na Afirka.

Janar Christopher Musa
Janar Christopher Musa a wajen baje kolin makamai. Hoto: GEN CG Musa
Source: Facebook

This Day ta wallafa cewa ministan ya bayyana hakan ne yayin buɗe baje kolin kayayyakin tsaro na ƙasashen Afirka, AFRIDEX, karo na farko, wanda aka gudanar a Legas.

Ministan ya yi kira ga mahalarta taron da su yi amfani da damar da baje kolin ya samar wajen zuba jari a masana’antun tsaro na Najeriya.

Ya bayyana cewa waɗannan shirye-shirye za su haɗa hukumomin tsaro, wakilan gwamnatoci, masu ruwa da tsaki a masana’antu da sauran abokan hulɗa masu muhimmanci.

A bayanin shi, ya ce manufar ita ce ƙarfafa haɗin gwiwa da samar da damar zuba jari da za su taimaka wajen bunƙasa masana’antun tsaro a Najeriya.

Muhimmancin baje kolin makamai

A nasa jawabin, ƙaramin Ministan Tsaro, Dr Bello Muhammad Matawalle, ya bayyana AFRIDEX a matsayin wata muhimmiyar kafa da za ta iya cimma manufofin da aka samar da ita domin su.

Bello Matawalle a a wajen taro.
Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle. Hoto: Bello Matawalle
Source: UGC

Premium Times ta rahoto ya ce taron zai ba wa masu ruwa da tsaki damar tattaunawa da musayar ra’ayoyi kan hanyoyin bunƙasa ɓangaren tsaro da masana’antunsa.

Kara karanta wannan

Matatar Dangote ta kafa tarihi bayan kammala sayar da hannayen jari

Gwamnan jihar Legas, wanda mataimakinsa, Dr Obafemi Hamzat, ya wakilta, da wakilin Hukumar ECOWAS, Birame Diop, sun bayyana fatan cewa taron zai samar da dama ga ƙasashen Afirka wajen faɗaɗa da farfaɗo da masana’antun tsaronsu.

An kama mai goyon bayan Atiku

A wani labarin, mun ruwaito cewa Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta gurfanar da wani mai goyon bayan tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, bisa zargin yaɗa wata takarda yi wa Bola Tinubu karya.

An kama wanda ake zargin, Mubarak Abdullahi, wanda aka fi sani da Sardaunan Samari, a ranar 28 ga Satumba bisa zargin ya wallafa takardar da ake zargin na bogi ce a shafinsa na Facebook.

A cewar sanarwar da Bayo Onanuga ya fitar ranar Litinin, Mubarak ya amince wa masu bincike cewa ya yaɗa takardar tare da neman afuwa kan abin da ya aikata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng