Iran: An Sauke Babban Sojan da ke yi wa Amurka Tsare Tsaren kai Farmaki
- Ministan tsaron Amurka, Pete Hegseth, ya sallami Laftanar Janar Brett Sylvia, wanda ke jagorantar tsare-tsare da manufofin dabarun sojin ƙasar
- Matakin ya zo ne yayin da suke nazarin kai sababbin hare-haren soji kan Iran, bayan rahotannin cewa dakarun Amurka a Gabas ta Tsakiya sun shirya
- Ba a bayyana dalilin sallamar Sylvia ko wanda zai gaje shi ba, yayin da matakin ya ƙara cikin jerin manyan jami’an sojin da suka bar muƙamansu a gwamnatin Trump
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Washington, Amurka – Ministan tsaron Amurka, Pete Hegseth, ya sallami babban jami’in da ke kula da tsare-tsare da manufofin dabarun sojin ƙasar, Laftanar Janar Brett Sylvia.
Wata majiya da ke da masaniya kan lamarin ce ta bayyana cewa an cire Sylvia daga muƙaminsa na daraktan tsare-tsare da manufofin dabarun rundunar hafsoshin sojin Amurka, wanda aka fi sani da J5.

Source: Getty Images
Mai magana da yawun shugaban rundunar hafsoshin sojin ƙasar, Janar Dan Caine, ya tabbatar wa CNN cewa Sylvia zai bar muƙamin, amma ba a bayyana dalilin cire shi ba.
Ba a fadi dalilin sallamar Sylvia ba
Sylvia ya kasance daraktan J5, muƙamin da ke da muhimmiyar rawa wajen tsara dabarun soji da shawarwari kan manufofin tsaron Amurka a ƙasashen duniya.
A cewar rundunar hafsoshin sojin Amurka, sashen J5 yana tsara shawarwari da tsare-tsaren da shugaban rundunar ke amfani da su wajen ba shugaban ƙasa da sauran manyan jami’an gwamnati shawara kan batutuwan tsaron ƙasa.
Har zuwa lokacin da aka fitar da rahoton, ba a bayyana wanda zai maye gurbin Sylvia ba. Haka kuma, an tuntuɓi ofishin Hegseth domin jin ta bakinsa kan matakin.
Bugu da kari, A yammacin ranar Laraba, an cire tarihin Sylvia daga shafin intanet na rundunar hafsoshin sojin Amurka.
Wani mai magana da yawun rundunar ya gode masa bisa shekaru 32 da ya yi yana yi wa ƙasar hidima, tare da yi masa fatan alheri a sabon matakin rayuwarsa.

Source: Getty Images
Maganar kai hari kan Iran
Sallamar Sylvia ta zo ne a lokacin da ake ci gaba da tattaunawa kan yiwuwar Amurka ta sake kai hare-haren soji kan Iran.
A cewar wasu jami’an Amurka, dakarun ƙasar da ke Gabas ta Tsakiya sun shirya gudanar da sababbin hare-hare, waɗanda ka iya zama manyan farmaki, cikin sa’o’i 96 bayan samun umarni daga Trump.
Wani jami’in ya bayyana cewa aikin zai kasance babba, yayin da wasu jami’ai na yanzu da waɗanda suka taɓa riƙe muƙamai a baya suka nuna cewa ana ci gaba da shirye-shiryen soja.
Wasu daga cikin jami’an sun yi hasashen cewa Trump na iya ba da umarnin kai harin kafin ƙarshen shekarar 2026, musamman bayan zaɓen tsakiyar wa’adin Amurka.
Sai dai rahoton ya ce Trump bai yanke shawara ta ƙarshe ba, kuma a baya ya taɓa nuna sha’awar ɗaukar wasu matakai kafin daga bisani ya fasa.
Rahoton CNBC ya nuna cewa Trump ya kuma bayyana a baya cewa ba za a kai wa Iran hari kafin zaɓen tsakiyar wa’adin ba.
Amurka ta kama 'yan Najeriya
A wani labari, mun ruwaito cewa Amurka sanar a kama mutane tara a Najeriya sakamakon wani farmaki da dakarun hukumar FBI ta gudanar.
An gudanar da samamen ne a ƙarƙashin wani shiri mai suna Operation Blackout, wanda aka mayar da hankali wajen tarwatsa cibiyoyin damfara.
Daraktan FBI, Kash Patel, ya ce jami’an sun kama mutum tara, sun ƙwace na’urorin lantarki 53, tare da gano kuɗaɗen da za a iya daskarar da su.
Asali: Legit.ng


