Jami'an FBI na Amurka Sun Shigo Najeriya Sun Cafke Mutum 9
- Hukumar Binciken Manyan Laifuffuka ta Amurka (FBI) ta ce ta kama mutane tara a Najeriya a wani samame kan masu aikata laifuffukan intanet na ƙasa da ƙasa
- Hukumar ta kuma kwace na’urorin lantarki guda 53 tare da gano kuɗin da suka kai dala miliyan 11 da za a iya daskararwa a ƙasashe daban-daban
- Daraktan FBI, Kash Patel, ya ce za su ci gaba da bin diddigin masu damfarar mutane ta intanet, ba tare da la’akari da ƙasar da suke aikata laifuffukansu ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Hukumar Bincike ta Amurka (FBI) ta sanar da kama mutane tara a Najeriya tare da kwace na’urorin lantarki guda 53 a wani samame da ta gudanar kan ƙungiyoyin masu aikata laifuffukan intanet na ƙasa da ƙasa.

Kara karanta wannan
Rashin imani: An ɗaure mutum 3 da ake zargi da sace ƙaramin yaro kuma suka kashe shi a Kano
Daraktan hukumar, Kash Patel, ya bayyana cewa samamen ya kuma taimaka wajen gano kuɗin da suka kai dala miliyan 11 da za a iya daskararwa a ƙasashe daban-daban.

Source: Twitter
Patel ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X ranar Lahadi, inda ya ce aikin na daga cikin ƙoƙarin tarwatsa ƙungiyoyin masu aikata laifi a intanet da ke damfarar Amurkawa.
FBI ta kama mutum 9 a Najeriya
Patel ya ce an gudanar da samamen ne ƙarƙashin wani aiki mai suna Operation Blackout, wanda aka ƙaddamar domin yaƙi da ƙungiyoyin masu aikata laifuffukan intanet da ke satar kuɗin jama’a.
Ya bayyana cewa samamen da aka gudanar a Najeriya ya haifar da kama mutane tara, kwace na’urorin lantarki 53 da kuma gano kuɗin da suka kai dala miliyan 11 da za a iya daskararwa a ƙasashe daban-daban.
Daraktan FBI ya ce cibiyoyin damfara na intanet suna cutar da mutanen suna kwashe kuɗin ajiyarsu, sannan suna gudanar da ayyukansu ta ƙasashe daban-daban domin guje wa hukuma.
Ya kuma yaba wa jami’an tsaron Najeriya da abokan hulɗar hukumar da ke Landan bisa haɗin gwiwar da suka bayar wajen gudanar da samamen.
Amurka ta yi gargaɗi
Shugaban FBI ya yi gargaɗin cewa Amurka za ta ci gaba da bin diddigin mutanen da ke aikata laifuffukan intanet, ko da kuwa a wace ƙasa suke gudanar da ayyukansu.
Patel ya ce masu aikata waɗannan laifuffuka ba za su tsira daga hukunci ba saboda suna gudanar da ayyukansu daga ƙasashen waje.
Ya bayyana cewa Operation Blackout na da nufin kai farmaki kai tsaye kan ƙungiyoyin masu aikata laifi ta intanet da ake zargi da satar biliyoyin daloli daga Amurkawa.
Sai dai Patel bai bayyana sunayen mutanen da aka kama ba, ko takamaiman wuraren da aka gudanar da kamen a Najeriya.

Source: Getty Images
Abokin Trump ya fadi zabe
A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban ƙasar Brazil, Luiz Inácio Lula da Silva, ya samu nasarar sake lashe zaɓen shugaban ƙasa bayan ya doke Flávio Bolsonaro, ɗan tsohon shugaban ƙasar, Jair Bolsonaro.
Lula ya samu kashi 51.8 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa, inda ya doke abokin hamayyar nasa da kusan ƙuri’u miliyan 4.4, inda ya kayar da mutumin Trump.
Nasarar ta kasance babban koma wa fagen siyasa ga Lula, wanda ya kasance a baya da ƙuri’u sama da miliyan 2 a zagayen farko na zaɓen, mako uku kafin zagaye na biyu.
Asali: Legit.ng
