Babbar Magana: Trump Ya Yi Maganar Kashe Shugabannin Iran
- Donald Trump na kasar Amurka ya yi magana kan kashe shugabannin Jamhuriyar Musulunci ta Iran
- Shugaban na Amurka ya yi ikirarin cewa hare-haren sojin Amurka sun raunana shugabanci da ƙarfin tsaron Iran sosai
- Trump ya kare matakin da ya ɗauka a 2018 na janye Amurka daga yarjejeniyar nukiliyar Iran, yana mai cewa ba zai bari Tehran ta mallaki makamin nukiliya ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Georgia, Amurka - Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce yana buƙatar dakatar da kashe shugabannin Iran.
Shugaba Trump ya ce yana bukatar dakatar da kashe shugabannin ne domin ya iya gano waɗanda ƙasarsa ke tattaunawa da su.

Source: Getty Images
Tashar Aljazeera ta kawo rahoton cewa Trump ya bayyana hakan ne yayin wani gangamin siyasa a jihar Georgia, a ranar Asabar, 24 ga watan Oktoban 2026.
Me Trump ya ce kan shugabannin Iran?
Ta sake jaddada adawarsa da mallakar makamin nukiliya da Iran, tare da ikirarin cewa hare-haren sojin Amurka sun raunana shugabanci da ƙarfin tsaron ƙasar sosai.
“Dole ne na dakata da kashe su, domin ina buƙatar gano waɗanda muke tattaunawa da su,” in ji Trump, yana magana kan shugabannin Iran.
Ya kuma yi ikirarin cewa an kashe manyan shugabannin Iran da dama, tare da lalata ko raunana kadarorin sojinta.
“Ba su da jiragen sama, ba su da jiragen ruwa, ba su da komai, ba su da shugabanni. An kawar da shugaba na mataki na ɗaya. An kawar da shugaba na mataki na biyu,” in ji shi.
Trump ya kare janye Amurka daga yarjejeniyar Iran
Trump ya kuma kare matakin da ya ɗauka a shekarar 2018 na janye Amurka daga yarjejeniyar nukiliyar Iran ta 2015, wadda aka cimma a lokacin mulkin tsohon shugaban Amurka, Barack Obama.
Yarjejeniyar, wadda aka fi sani da Joint Comprehensive Plan of Action (JCPOA), an tsara ta ne domin takaita ayyukan nukiliyar Iran tare da sanya ido a kansu, a musayar sassauta takunkuman tattalin arziki.
Trump ya bayyana yarjejeniyar a matsayin wata yarjejeniya mara kyau da ta iya bai wa Iran damar mallakar makamin nukiliya.
“Na soke ɗaya daga cikin yarjejeniyoyin da suka fi muni da aka taɓa yi, wato yarjejeniyar nukiliyar Barack Hussein Obama, ko kuma kamar yadda wasu ke kiranta, yarjejeniyar nukiliyar Iran. Hanya ce da za ta kai Iran ga mallakar makamin nukiliya. Na soke ta, kuma cikin sa’a na yi hakan a kan kari,” in ji shi.
Ya yi ikirarin lalata karfin nukiliyar Iran
Trump ya kuma yi ikirarin cewa hare-haren sojin Amurka sun lalata ƙarfin Iran na tace sinadaran nukiliya, yana ambaton hare-haren da ya kira Operation Midnight Hammer da Operation Epic Fury.
Ya ce Amurka ta yi galaba a kan Iran ta fuskar soja, kuɗi da sauran fannoni, yana mai jaddada cewa dole ne a hana ƙasar mallakar makamin nukiliya har abada.
“Mun lalata ƙarfin Iran na tace sinadaran nukiliya ta hanyar Operation Midnight Hammer da Operation Epic Fury.

Kara karanta wannan
Atiku ko Tinubu: An raba gardama kan dan takarar da ya fi dacewa ya zama shugaban kasa
“Mun yi galaba a kansu ta fuskar soja, kuɗi da sauran fannoni. Dole ne mu tabbatar da cewa ba za su taɓa mallakar makamin nukiliya ba.” In ji shi

Source: Getty Images
Amurka da Israila na shirin kai hari a Iran
A wani labarin kuma, kun ji cewa sojojin Amurka da Isra’ila sun tsara wasu takamaiman tsare-tsaren sake kai hare-hare kan Iran bayan zaɓen tsakiyar wa’adin Amurka.
Wasu jami’an Amurka da wasu mutanen da aka sanar da su bayanan tattaunawar shirye-shiryen sojoji suka bayyana hakan.
Asali: Legit.ng

