Mummunan Hatsarin Mota Ya Ritsa da Tawagar Gwamna Bago, an Samu Asarar Rayuka
- Mutane uku sun rasa rayukansu a hatsarin mota da ya faru a Gidan Mangoro da ke kan hanyar Minna zuwa Bida a jihar Neja
- Wata motar Hilux da ke cikin tawagar Gwamna Mohammed Umaru Bago ce ta yi karo da wata mota yayin da gwamnan ke dawowa daga Bida
- Wani mazaunin yankin ya yi zargin cewa kuskuren wuce wata mota ne ya haddasa hatsarin, yayin da jami’an FRSC suka tabbatar da faruwar lamarin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Neja - Mutane uku sun mutu a wani hatsarin mota da ya faru a al’ummar Gidan Mangoro, da ke kan hanyar Minna zuwa Bida a jihar Neja.
Hatsarin ya faru ne ranar Litinin, 26 ga watan Oktoban 2026 bayan wata motar Hilux da ke cikin tawagar Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ta yi karo da wata motar gida da ke tafiya.

Source: Twitter
Wani mazaunin Gidan Mangoro, Danjuma Umar, ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa hatsarin ya faru ne da misalin karfe 11:00 na safe, a lokacin da gwamnan ke dawowa daga garin Bida.
Ya ce ana zargin mutanen da ke cikin motar gidan dalibai ne masu yin digiri na biyu a Jami’ar Fasaha ta Tarayya da ke Minna (FUT Minna).
A cewarsa, dukkan mutanen da ke cikin motar gidan sun mutu nan take, yayin da wadanda ke cikin motar Hilux suka samu munanan raunuka.
Me ake zargin ya haddasa hatsarin?
Danjuma ya yi zargin cewa direban motar Hilux ne ya haddasa hatsarin sakamakon wuce wata mota ba bisa ka’ida ba.
Ya ce motar gidan tana kan layinta ne lokacin da motar Hilux ta kutsa ta bangarenta, ta yi karo da ita.
Danjuma ya kuma bayyana cewa wata mata ce ke tuka motar gidan, wadda mazauniyar kauyen Gidan Mangoro ce.

Kara karanta wannan
InnalilLahi wa inna ilaihi raji'un, an kashe Sheikh Yahaya Masussuka a ƙofar gidansa
Mutum 3 sun mutu, wasu sun samu raunuka
Wani ma’aikacin Babban Asibitin Minna ya bayyana cewa an kai gawarwakin mutane biyu asibitin, yayin da mutum na uku ya rasu a sashen gaggawa na asibitin, inda aka kwantar da shi domin jinya.
Rahoton ya ce an tura wasu daga cikin wadanda suka jikkata zuwa Asibitin Kwararru na IBB domin samun kulawar likitoci ta musamman.
Haka kuma, an tattaro cewa daya daga cikin mutanen da ke cikin motar Hilux tsohon shugaban karamar hukuma ne, wanda ya samu karaya a kafafunsa.
FRSC ta tabbatar da faruwar hatsarin
Kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) a jihar Neja, Aishat Sa’adu, ta tabbatar da faruwar hatsarin.
Sai dai ta ce kafin jami’an hukumar su isa wurin, an riga an kwashe wadanda hatsarin ya rutsa da su.
Aishat Sa’adu ta tabbatar da cewa akwai wadanda suka mutu ko suka jikkata, amma ba ta iya bayyana adadin mutanen da hatsarin ya shafa ba.

Source: Original
Tsohon shugaban APC ya yi hatsari
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shigaban jam'iyyar APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas ya gamu da hatsarin mota.
Abdullahi Abbas ya gamu da hatsarin ne a hanyar komawa gida bayan halartar taron kaddamar da yakin neman zaben APC a Kano.
Asali: Legit.ng

