Mutane Sun Fada Kogi yayin Gudun Tsira daga 'Yan Bindiga, an Samu Gawa 50

Mutane Sun Fada Kogi yayin Gudun Tsira daga 'Yan Bindiga, an Samu Gawa 50

  • Adadin mutanen da ’yan bindiga suka kashe a harin da suka kai garin Binnari da ke Jihar Taraba ya kai aƙalla 50, bayan gano wasu gawarwaki a cikin kogi
  • Shaidu da suka gana da Amnesty International sun ce wasu daga cikin waɗanda suka mutu sun nutse ne yayin ƙoƙarin tserewa daga hannun maharan
  • ’Yan sanda sun ce suna ci gaba da bincike a yankin, yayin da Amnesty International ta yi kira ga hukumomi su ɗauki mataki kan matsalar hare-haren ’yan bindiga

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Adadin mutanen da ’yan bindiga suka kashe a harin da suka kai garin Binnari da ke gabashin Jihar Taraba ya ƙaru zuwa aƙalla 50, bayan gano ƙarin gawarwaki a cikin kogi.

Kara karanta wannan

Manyan Saudiyya da na kasashen Musulmi 2 sun tafi Iran taron tsaro

Rahoton ya nuna cewa waɗanda suka tsira daga harin da ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Amnesty International sun tabbatar da ƙarin adadin waɗanda suka mutu.

Gwamnan jihar Taraba
Gwamnan Taraba, Agbu Kefas. Hoto: Taraba State Government
Source: Twitter

BBC ta wallafa cewa maharan da ake zargin ’yan bindiga ne, sun shiga garin ne a kan babura jim kaɗan bayan sallar Juma’a, inda suka kashe mutane da dama, tare da wawushe kayayyaki da ƙona shaguna.

An gano gawa 43 a kogi

Wani mazaunin garin Binnari, Bashir Mamuda Musa, ya shaida cewa an gano gawa bakwai a ranar Juma’a bayan harin.

Ya ce a ranar Asabar, an sake gano wasu gawa 43 a cikin kogi, abin da ya sa adadin waɗanda aka gano gawarwakinsu ya kai 50.

Wani mazaunin yankin, Abdullahi Zakari, shi ma ya tabbatar da wannan adadi.

Zakari ya ce mazauna garin da dama, ciki har da mata da yara, sun gudu zuwa wajen kogin domin tsira daga maharan, amma wasu sun nutse a lokacin ƙoƙarin tserewa.

’Yan sanda na neman gawa

Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jihar Taraba, Victor Msheliza, ya shaida cewa jami’an tsaro na ci gaba da bincike a yankin domin gano sauran waɗanda harin ya shafa.

Kara karanta wannan

Ana zargin dan sanda ya bude wuta a wajen Maulidi, ya yi kisan kai

Ya ce jami’an ’yan sanda sun gano wasu gawarwaki a cikin kogin, waɗanda ake zargin sun nutse ne yayin ƙoƙarin tserewa daga maharan.

Msheliza ya ƙara da cewa an tura jami’an tsaro yankin nan take bayan faruwar harin, kuma ana aika ƙarin jami’ai domin ƙarfafa tsaro.

A nata ɓangaren, Amnesty International ta ce adadin waɗanda suka mutu ya kai 52, tana mai cewa maharan sun zo da yawa tare da ƙona shaguna da rumfunan kasuwa.

Shugaban Amnesty International a Najeriya, Isa Sanusi, ya ce wasu daga cikin mazauna yankin sun nufi kogi ne domin tsira, amma maharan sun bi su har cikin ruwan, inda wasu suka nutse.

Taswirar jihar Taraba
Taswirar jihar Taraba a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

A cikin wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X, Amnesty International ta zargi hukumomin Najeriya da barin wasu al’ummomin karkara cikin halin rashin kariya daga ’yan bindiga da ke ci gaba da aikata ta’asa ba tare da fuskantar hukunci ba.

An kashe matashi a Borno

A wani labarin, mun ruwaito cewa ƙungiyar Amnesty International ta yi kira ga hukumomin Najeriya da su gudanar da bincike kan zargin kashe wani matashi mai suna Umar Muhammad a wajen Mauludi a Borno.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun yi amfani da tafiya kamfen Tinubu, sun tafka mummunan ta'adi a Zamfara

Ƙungiyar ta yi kiran ne a wani saƙo da ta wallafa, inda ta bayyana lamarin a matsayin zargin kisan kai ba bisa ƙa’ida ba, tare da buƙatar a ɗauki mataki kan mutuwar matashin.

A cewar Amnesty International, shaidu sun bayyana cewa jami’an ’yan sanda ƙarƙashin jagorancin wani jami’in mai muƙamin sufeto sun fara zuwa wurin taron addinin ne domin korafi kan ƙarar lasifikan da ake amfani da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng