Babbar Magana: An Yi Barazanar Fitar da Hotunan Tsiraicin Gwamna Abba

Babbar Magana: An Yi Barazanar Fitar da Hotunan Tsiraicin Gwamna Abba

  • Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin tsare Sanusi Dankaka a Kuje bayan an gurfanar da shi kan tuhume-tuhume biyu na laifuffukan yanar gizo
  • DSS ta zargi Dankaka da ikirarin cewa yana da bidiyo da hotunan tsiraicin Gwamnan Kano, Abba Yusuf, tare da barazanar wallafa su a Facebook
  • Dankaka ya musanta dukkan tuhume-tuhumen, yayin da kotun ta dage sauraron shari’ar zuwa ranar 7 ga Disamba domin fara shari’a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin tsare Sanusi Dankaka a gidan gyaran hali na Kuje, kan zargin barazana ga Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano.

An bayar da umarnin ne bayan an gurfanar da shi kan zargin yi wa Gwamna Abba Kabir Yusuf, barazanar wallafa bidiyo da hotunansa na tsiraici a Facebook.

Kara karanta wannan

Rashin imani: An ɗaure mutum 3 da ake zargi da sace ƙaramin yaro kuma suka kashe shi a Kano

Matashi ya yi barazana ga Gwamna Abba
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jawabi a wajen taro Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

An yi wa Gwamna Abba barazana

Jaridar Leadership ta ce mai shari’a Salim Ibrahim ne ya bayar da umarnin a ranar Litinin, 26 ga watan Oktoban 2026 bayan Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta gurfanar da Dankaka bisa tuhume-tuhume biyu da suka shafi zargin aikata laifukan yanar gizo.

Sai dai wanda ake tuhumar ya musanta dukkan zarge-zargen da ake yi masa dangane da gwamnan na jihar Kano.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa DSS ta shigar da karar mai lamba FHC/ABJ/CR/699/2026 a ranar 22 ga Oktoba, ta hannun lauyanta, Yusuf Afegbua.

DSS ta bayyana zargin da ake yi wa Dankaka

A cewar masu gabatar da kara, an aikata laifuffukan da ake zargin Dankaka da su ne a watan Oktoban 2026, a karamar hukumar Jos ta Arewa, da ke jihar Plateau.

A tuhuma ta farko, DSS ta zargi Dankaka da wasu mutanen da ake cewa har yanzu ba a kama su ba da yunkurin yada abubuwan da ake zargin na da illa ta wani asusun Facebook mai suna Sanusi Dankaka Yahaya.

Kara karanta wannan

Kotu ta ba El Rufai sabon umarni bayan kin amincewa da bukatarsa

Hukumar ta yi ikirarin cewa Dankaka ya bayyana cewa yana da bidiyo da hotunan tsiraicin Gwamna Abba Kabir Yusuf, sannan ya yi barazanar fitar da su ga jama’a.

DSS ta kuma yi zargin cewa bayanan da ake shirin wallafawa na karya ne, kuma an yi hakan ne da nufin bata wa gwamnan rai, jawo masa rashin jin dadi, zagi ko cutar da shi.

Masu gabatar da kara sun ce zargin ya sabawa sashe na 27(1)(b) na dokar hana aikata laifukan yanar gizo ta shekarar 2015, kamar yadda aka yi wa dokar kwaskwarima, kuma hukuncin da ya dace yana karkashin sashe na 24(1) na dokar.

Dankaka ya musanta tuhume-tuhumen

Lokacin da aka kira karar a ranar Litinin, lauyan DSS, Yusuf Afegbua, ya shaida wa kotu cewa bangaren masu gabatar da kara a shirye yake domin a fara shari’ar.

Lauyar wanda ake tuhuma, Kauna Penzin, ita ma ta tabbatar da cewa a shirye take domin gudanar da shari’ar.

Bayan an karanta wa Dankaka tuhume-tuhumen da ake yi masa, ya bayyana cewa ba shi da laifi kan dukkan zarge-zargen.

Daga nan ne Afegbua ya nemi kotu ta sanya ranar fara shari’ar tare da bayar da umarnin tsare wanda ake tuhuma a gidan gyaran hali na Kuje har zuwa lokacin da za a ci gaba da sauraron karar.

Kara karanta wannan

Zargin badala: Hukumar Hisbah ta cafke fitacciyar 'yar TikTok a Kano

An dage shari’ar zuwa 7 ga Disamba

Mai shari’a Ibrahim ya amince da bukatar masu gabatar da kara, inda ya umarci a ci gaba da tsare Dankaka a Kuje har zuwa zaman kotu na gaba.

Kotun ta dage shari’ar zuwa ranar 7 ga Disamba domin fara sauraron karar.

An yi wa Gwamna Abba barazana
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Gwamna Abba ya yi magana kan zaben 2027

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya bukaci mambobin kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da na gwamna na APC da su yi aiki tukuru.

Gwamna Abba ya bukaci su tashi tsaye domin tabbatar da cewa Kano ta samar da mafi yawan ƙuri’u ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu a babban zaɓen shekarar 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng