Gwamnan Katsina Ya Fadi Matakin da za a Dauka kan Kashe Masussuka
- Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya yi jimamin kisan malamin addinin Musulunci, Sheikh Yahaya Masussuka, wanda wasu ’yan bindiga suka kashe a Dutsin-Ma
- Radda ya bayyana marigayin a matsayin malamin da ya yi fice wajen wa’azin zaman lafiya, zaman tare tsakanin mabiya addinai musamman a Arewacin Najeriya
- Gwamnan ya yi alƙawarin gudanar da cikakken bincike kan kisan, tare da kira ga mazauna jihar da su kwantar da hankalinsu su kuma bai wa jami’an tsaro haɗin kai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Katsina – Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya yi jimamin kisan Sheikh Yahaya Masussuka, tare da alƙawarin cewa za a gudanar da cikakken bincike domin gano waɗanda suka aikata laifin.
Rahotanni sun bayyana cewa wasu ’yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kashe malamin da wani abokinsa a wajen gidansa da ke ƙaramar hukumar Dutsin-Ma a daren ranar Litinin, 26 ga Oktoba, 2026.

Kara karanta wannan
InnalilLahi wa inna ilaihi raji'un, an kashe Sheikh Yahaya Masussuka a ƙofar gidansa

Source: Facebook
Mai magana da yawun gwamnatin Katsina, Ibrahim Kaulaha Muhammad ne ya fitar da sanarwa a madadin gwamnan a sakon da ya wallafa a Facebook.
Gwamna Radda ya yi ta'aziyya
Gwamna Radda ya bayyana kaduwarsa kan kisan, inda ya mika ta'aziyyarsa ga iyalan marigayin, al'ummar Musulmi da sauran waɗanda wannan rashi ya shafa.
Ya bukaci iyalan da su yi haƙuri, su kuma jingina al'amuransu ga Allah Madaukakin Sarki a wannan lokaci mai cike da baƙin ciki.
Radda ya ce:
“Ina kira ga iyalan mamacin da su yi haƙuri da ƙaddarar Allah Madaukakin Sarki, su kuma tsaya tsayin daka wajen riƙe imaninsu a wannan lokaci mai wahala. Allah Ya ba su ƙarfi da haƙurin jure wannan babban rashi.”
Za a yi binciken kashe Masussuka
Gwamnan ya tabbatar da cewa jami’an tsaro za su ƙara ƙaimi wajen gudanar da bincike kan kisan, gano waɗanda suka aikata shi da kuma gurfanar da su a gaban shari’a.
Ya jaddada cewa ba za a bar waɗanda ke da hannu a kisan su kuɓuta daga hukuncin doka ba.
Radda ya ce:
“Dole ne a gurfanar da waɗanda suka aikata wannan mummunan aiki a gaban shari’a. Ina kira ga hukumomin tsaro da abin ya shafa da su gudanar da cikakken bincike, tare da tabbatar da cewa waɗanda suka aikata laifin sun fuskanci hukuncin da doka ta tanada.”
Ya kuma yi kira ga mazauna jihar da su kwantar da hankalinsu, su ba jami’an tsaro haɗin kai tare da kai musu sahihan bayanan da za su taimaka wajen gudanar da binciken.

Source: Original
Gwamnan ya gargaɗi jama’a kan ɗaukar matakan da ka iya ƙara tayar da hankali ko kawo cikas ga zaman lafiya.
An kashe mutane a Taraba
A wani labarin, mun ruwaito cewa adadin mutanen da ’yan bindiga suka kashe a wani hari da suka kai a Karim Lamido a jihar Taraba ya kai aƙalla 50
Rahotanni sun bayyana cewa maharan, waɗanda ake zargin ’yan bindiga ne, sun shiga garin Binnari da ke gabashin jihar Taraba a kan babura suka kashe jama'a.
Wasu mazauna yankin sun ce an gano gawa bakwai a ranar Juma’a, yayin da aka gano wasu 43 a cikin kogi washegari, lamarin da ya tada hankali.
Asali: Legit.ng
