"A Yafe Mana," Kamfanin MTN Ya ba da Haƙuri kan Karin Farashin 'Data'
- Kamfanin sadarwa na MTN ya gaggauta ba jama'a haƙuri biyo bayan karin kuɗin 'data' da akalla 200% a tsakiyar makon nan
- MTN ya lura da yadda jama'a su ka yi masa ca a kafafen sada zumunta, wanda hakan ya sa ya fitar da sako domin kwantar da hankula
- A ranar Alhamis ne dai kamfanin ya fitar da sabon farashin 'data, kuma 15GB da ake saye a ₦2,000 ya tashi zuwa ₦6,000
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Kamfanin sadarwa, MTN, ya ba da hakuri ga abokan huldarsa a matsayin martani ga fushin jama'a a kan ƙarin farashin data da ya yi
Jama'a sun wayi gari da ganin cewa kamfanin ya ƙara kuɗin data ta 15GB da akalla 200%, da ma sauran ƙare-ƙaren farashin data.

Asali: Twitter
A sakon da ta aka wallafa a shafin X na MTN, kamfanin ya ce yana sane da yadda ƙarin farashin bai yi wa abokan huldarsu dadi ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƙarin farashin, na nufin data na mako-mako na 15GB ya tashi daga N2,000 zuwa N6,000, kuma hakan ya jawo ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta.
Kamfanin MTN ya ba 'yan Najeriya hakuri
Daga cikin kalaman haƙuri da sanyaya zuciya da MTN ya yi wa abokan huldarsa na Najeriya, kamfanin ya amince da cewa ya 'kwafsa', amma a yi hakuri.
Sakon ya ce:
"Ga masoya da ke amfani da 150 na tsarin data, kuna cikin fushi. Mun san haka.
"Mun san da ciwo sosai idan ka tashi kwatsam da hauhawar farashin 200% a kan tsarin data da ka fi so.
"Ba za mu iya kare kanmu ba, amma mun yi kuskure. Mun fahimta kuma mun amince da shi. A ce kawai kuskure ne."

Kara karanta wannan
"Tinubu zai sha wahala": LP ta bayyana wanda za ta tsayar takarar shugaban ƙasa a 2027
MTN ya jinjina wa abokan hulda
A sakon na MTN, kamfanin ya ce yana matuƙar jin daɗin mu'amala da abokan hulɗarsa, kuma zai so a ci gaba da hulɗa kamar yadda ake yi a baya.
Sakon ya ce:
A wannan lokacin na soyayya, ka da ku ci gaba da fushi da mu. Don Allah ku yafe kuma ku manta. Kuna da muhimmanci sosai kuma ba za mu taɓa daina nuna muku yadda muke ƙaunar ku ba. Mu ci gaba da dangantaka."
'Ƴan Najeriya sun yi tir da ƙarin kuɗin 'data'
A baya, mun wallafa cewa kungiyar masu amfani da layukan sadarwa (NATCOMS) ta nuna rashin amincewa da karin kudin tarho da 'data' a Najeriya.
Kungiyar ta bayyana damuwarta tana mai cewa karin kudin bai dace ba a wannan lokaci, kuma zai kara wa mutane wahalhalu da ake fama da shi yanzu a kasar.
A baya, kamfanonin sadarwa, ciki har da MTN, sun nemi karin 100% saboda tsadar aiki da karin kudi a wasu fannoni, suna ganin hakan zai inganta ayyukansu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng