Shugaba Buhari Ya Buƙaci Kamfanin MTN Ya Rage Farashin 'Data' Ga Yan Najeriya

Shugaba Buhari Ya Buƙaci Kamfanin MTN Ya Rage Farashin 'Data' Ga Yan Najeriya

  • Shugaba Buhari ya roƙi kamfanin sadarwa na MTN ya sauƙaƙa wa yan Najeriya masu amfani da layukan su
  • Buhari yace Najeriya ce ƙasa ta uku a duniya da kamfanin ya fi samun kuɗaɗen shiga
  • Kamfanin ya sha alwashin yin duk me yuwu wa domin samar da ingantaccen sabis a Najeriya

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya yi kira ga kamfanin sadarwa na MTN da su rage farashin sayen 'Data' ga yan Najeriya, kamar yadda the cable ta ruwaito.

Buhari yayi wannan kira ne yayin da ya karɓi baƙuncin shugabannin kamfanin, ƙarkashin jagorancin shugaban MTN, Ralph Mupita, a fadar sa dake Abuja.

KARANTA ANAN: PDP Ta Ragargaji APC a Zaɓen Cike Gurbin da Aka Gudanar a Jihar Kaduna

Buhari ya tabbatar wa kamfanin MTN cewa gwamnatinsa zata yi duk me yuwu wa domin samar da kyakkyawan wuri na yin kasuwanci a Najeriya.

Buhari, Pantami da shugabannin MTN
Shugaba Buhari Ya Buƙaci Kamfanin MTN Ya Rage Farashin 'Data' Ga Yan Najeriya Hoto: @muhammadubuhari
Asali: Instagram

Buhari yace: "Najeriya ce ƙasar da kuka fi samun garabasar kasuwanci a Africa, Asia da sauran su, kuma ita ce ƙasa ta uku da kamfanin MTN yafi samun kuɗin shiga. Sabida haka, muna roƙon ku, ku sauƙaƙa wa yan Najeriya masu amfani da MTN."

KARANTA ANAN: Mu Haɗu a Filin Yaƙi, Gwamna Yayi Alƙawarin Shiga Daji Domin Yaƙi da Yan Bindiga

MTN yace za'a samu ƙasarancin sabis sabida matsalar tsaro

A ranar laraba, shugaban MTN Nigeria, Karl Toriola, ya bayyana cewa kwastomomi ka iya fuskantar karancin sabis a Najeriya saboda ƙaruwar matsalar tsaro.

Kamfanin sadarwar na MTN ya kara da cewa zai yi iyakacin ƙoƙarinsa ya tabbatar da an samu ingantaccen sabis da zai wa yan Najeriya aiki yadda suke buƙata.

A wani labarin kuma Sojoji Sun Kashe Yan Bindigan da Suka Sace Ɗaliban FGC a Kebbi Sama da 80

Sojoji sun kashe yan bindiga sama da 80, waɗanda suka sace ɗaliban makarantar FGC Birnin Yauri, kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.

Shaidu sun bayyana cewa jami'an sojin sun yi amfani da dabarar yaƙi, inda suka yi wa ɓarayin kofar rago.

Asali: Legit.ng

Online view pixel