An Dauke Matar da Ta Shigo da Ebola Najeriya, Ta Bar Abuja zuwa Kasar Waje

An Dauke Matar da Ta Shigo da Ebola Najeriya, Ta Bar Abuja zuwa Kasar Waje

  • An dauke majinyaciyar cutar Ebola ta farko da aka tabbatar a Najeriya zuwa Switzerland domin ci gaba da jinya
  • Matar mai shekaru 42 da ta kamu da nau’in kwayar cutar Ebola ta Bundibugyo, an ɗauke ta an bar Najeriya da misalin karfe 6:00 na safiyar Litinin
  • Hukumomin lafiya sun gano mutane 53 da suka yi mu’amala da majinyaciyar, inda aka killace su tare da ci gaba da sa ido kan lafiyarsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Rahotanni sun nuna cewa an dauke matar da aka gano tana da cutar Ebola ta farko da aka tabbatar a Najeriya zuwa kasar Switzerland domin ci gaba da jinya.

An ɗauki matar mai shekaru 42, wadda aka tabbatar ta kamu da nau’in cutar Ebola mai suna Bundibugyo, da jirgin sama na musamman da misalin ƙarfe 6:00 na safiyar Litinin daga filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Najeriya ta samu sauki kan cutar Ebola bayan sabon matakin da aka dauka

Likitoci.
Likitocin da ke kula da masu dauke da cutar Ebola Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Majinyaciyar Ebola ta bar Najeriya

The Cable ta ruwaito cewa Aman ɗauko majinyaciyar, wadda matar wani jami’in diflomasiyyar Switzerland ce, daga tsakiyar birnin Abuja a cikin ayarin motocin asibiti.

Motocin diflomasiyya sun shiga yankin filin jirgin saman da aka ajiye jiragen sama masu zaman kansu, inda daga nan aka sanya ta a jirgi zuwa kasar Switzerland.

Wannan na zuwa ne yayin da hukumomin lafiya ke ƙara tsaurara matakan gano mutanen da suka yi mu’amala da majinyaciyar, inda aka gano mutane 53 da ke da alaƙa da wanda aka tabbatar ya kamu da cutar, tare da killace su.

Gwamnatin tarayya ta tabbatar

Ministan Lafiya da Jin Daɗin Jama’a, Ali Pate, ya tabbatar da cewa majinyaciyar ta bar Abuja zuwa Switzerland tare da mijinta, wanda har yanzu bai nuna alamun cutar ba.

“Na tabbatar da cewa, bisa amincewata, majinyaciyar da aka fara tabbatar da cewa ta shigo da cutar Ebola Najeriya ta tashi daga Abuja zuwa Switzerland da safiyar yau,” in ji Pate a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X ranar Litinin.

Kara karanta wannan

'Yan daba sun farmaki ayarin ɗan takarar jam'iyyar su Kwankwaso, an kashe mutum 1

Pate ya ce yanayin lafiyar majinyaciyar ya inganta sosai, tana cikin kwanciyar hankali, cikin hayyacinta kuma tana iya magana da mutane.

Matar ta fara warkewa daga cutar

Ya ƙara da cewa sakamakon gwaje-gwajen jininta na dakin gwaje-gwaje ya kusa komawa yadda yake kafin ta kamu da cutar.

Sai dai ya lura cewa samun sauƙin lafiya ba yana nufin majinyaciyar ta daina iya yaɗa cutar ba, don haka ana ci gaba da bin ƙa’idojin kariya da matakan lafiyar jama’a.

Ali Pate.
Ministan harkokin lafiya na Najeriya, Muhammad Ali Pate a ofis a Abuja Hoto: @muhammadpate
Source: Twitter

Ministan ya yaba wa ma’aikatan lafiya da suka kula da majinyaciyar da kuma jami’an lafiyar jama’a da suka tsara kwashe ta bisa ƙa’idojin tsaro da aka tanada.

Ya ƙara da cewa za a fitar da ƙarin bayani bayan majinyaciyar da mijinta sun isa inda za su je lafiya.

Pate ya kuma tabbatar wa ’yan Najeriya cewa ana ci gaba da aiwatar da matakan kare lafiyar jama’a domin shawo kan cutar da aka shigo da ita ƙasar.

Dalilin rashin samar da rigakafin Ebola

Kun ji cewa shugaban hukumar CDC ta nahiyar Afirka ya yi magana kan rashin samar da magani/rigakafin nau'in cutar Ebola da ta shiga Najeriya.

Ya ce nuna halin ko in kula na kasashen duniya ne ya sa har yau babu rigakafin da aka amince da shi kan nau’in cutar Ebola ta Bundibugyo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262