Duk da Ƙoƙarin Tinubu kan Tsadar Kaya, Abinci na Ci Gaba da Tashi a Kasuwanni

Duk da Ƙoƙarin Tinubu kan Tsadar Kaya, Abinci na Ci Gaba da Tashi a Kasuwanni

  • Duk da matakan da gwamnatin tarayya ke ɗauka don rage tsadar kayan noma da abinci, farashin kayan abinci na ci gaba da tashi a Najeriya
  • Manoma sun danganta tsadar abinci da hauhawar kuɗin sufuri, rashin tsaro, ƙarancin wuraren ajiya da jinkirin raba kayan tallafin noma ga manoma
  • Masana harkar noma sun buƙaci gwamnati ta saka jari a wuraren ajiyar amfanin gona masu amfani da hasken rana domin rage asarar abinci da tsadar kayayyaki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Duk da matakan da gwamnatin tarayya ta ɗauka domin rage tsadar kayan aikin gona da kuma farashin abinci, kayan abinci na ci gaba da tsada a Najeriya, har a lokacin girbi.

Manoma, ƙungiyoyin kasuwancin noma, ’yan kasuwa da masu sayen abinci sun danganta lamarin da tsadar sufuri, jinkirin rabon kayan tallafin noma, ƙarancin wuraren ajiya da rashin tsaro a wasu yankunan noma.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta ɗauko hanyar gyara, za a samu rangwamen tsadar rayuwar kwana 90

Farashin abinci na kara hauhawa a Najeriya
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Source: Twitter

Gargaɗin da manoma suka yi a bana

Sun yi gargaɗin cewa ƙara yawan amfanin gona kaɗai ba zai tabbatar da sauƙin farashi ba idan manoma ba za su iya adana amfanin gonarsu, kai shi kasuwanni cikin sauƙi ko samun kayan noma a lokacin da ya dace ba, cewar Punch.

Shirin Renewed Hope na Shugaba Bola Tinubu ya yi alƙawarin ƙarfafa samar da isasshen abinci, ƙara yawan amfanin gona a cikin gida, tallafa wa manoma da rage dogaro da kayan abinci daga ƙasashen waje.

A shekarar 2023, gwamnatin tarayya ta ayyana dokar ta-ɓaci kan samar da abinci, tare da sanar da shirin kashe naira biliyan 200 wajen noma hekta 500,000.

Shirin ya haɗa da raba takin zamani, iri da sauran kayan aikin gona domin ƙara samar da abinci da rage ƙarancinsa a kasuwanni.

Tun daga lokacin, gwamnatin ta sanar da wasu shirye-shirye, ciki har da tallafin injinan noma da raba takin zamani.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro ya yi kamari, limaman masallatan Juma'a sun yi magana da murya 1

A watan Yunin 2026, Asusun Bunƙasa Noma na Ƙasa (NADF) ya ƙaddamar da shirin raba buhunan takin zamani 515,720 ga manoma masu ƙananan gonaki 128,930 a jihohi 25 da Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Gwamnatin ta kuma bayyana matakan da za ta ɗauka domin tallafa wa samar da takin zamani a cikin gida, inganta samun kayan aikin gona da ƙara yawan amfanin gona.

Sai dai ƙungiyoyin manoma na nuna shakku kan tasirin waɗannan matakai, suna cewa tallafin ba ya isa ga manoman da suka cancanta a wasu lokuta, kuma ba ya haifar da raguwar farashin abinci.

Ana samun tashin farashin kayan abinci a Najeriya
Masu sayar da kayan abinci sun kasa hajarsu a kasuwa. Hoto: Pius Utomi Ekpei/Kola Sulaimon.
Source: Getty Images

Abin da hukumar NBS ta bayyana

Bayanan rahoton Ma’aunin Farashin Kayayyaki na Masu Sayayya (CPI) na watan Satumban 2026 da Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) ta fitar sun nuna cewa hauhawar farashin abinci a shekara ya kai kashi 19.59 cikin 100.

Wannan ya ɗan haura kashi 19.57 da aka samu a watan Agusta, amma ya yi ƙasa da kashi 20.16 da aka samu a watan Satumban 2025.

Hukumar ta danganta sauyin farashin da kayayyaki da suka haɗa da garin dawa, garin farin masara, shinkafa ta gida mai gajeren hatsi, ƙwai, albasa, man ja, koren wake, dankalin turawa, okra, tumatir, busasshen wake da plantain.

Kara karanta wannan

Tinubu zai fara karɓar harajin 25% daga kuɗaɗen shigan ƴan Najeriya?

A wata-wata, ma’aunin farashin abinci ya ragu da kashi 1.55 cikin 100 a watan Satumba, sabanin ƙarin kashi 1.02 da aka samu a watan Agusta.

Bayanan hauhawar farashin abinci a jihohi sun nuna cewa Lagos ce ta fi tsadar abinci, da kashi 34.40 cikin 100 a shekara.

Ƙungiyoyin manoma sun yi martani

Mataimakin shugaban ƙasa na Ƙungiyar Manoma ta Najeriya (AFAN), Daniel Okafor, ya ɗora alhakin tsadar abinci kan hauhawar farashin man fetur da rashin kyawun hanyoyi.

Ya ce waɗannan matsaloli sun ƙara kuɗin sufuri da sauran kuɗaɗen kai kayan abinci kasuwa.

Okafor, wanda kuma shi ne shugaban Ƙungiyar Manoman Dankalin Turawa ta Najeriya (POFAN), ya ce rashin tsaro a wasu yankunan noma yana hana manoma gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

Farashin abinci ya zube - Fadar shugaban kasa

A baya, an ji cewa Fadar shugaban ƙasa ta ce farashin kayan abinci ya ragu sosai, inda ta bayyana cewa buhun shinkafa ya yi kasa sosai.

Bayo Onanuga ya ce hauhawar ajiyar kuɗaɗen waje da ƙarin jarin ƙasashen waje na nuna cewa sauye-sauyen tattalin arzikin Tinubu.

Duk da ikirarin gwamnati, har yanzu ’yan Najeriya na nuna damuwa kan tsadar rayuwa, yayin da farashin kayan abinci ya bambanta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.