Nadin Sarki Ya Zo da Gardama, Gwamna Ya Ki Canza Shawara duk da Adawar Jama’a
- Oba Adesoye Adebowale Jimoh, ya bada labarin yadda Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya nada shi a shekarar 2024
- Gwamnan ya ki sauya nadinsa duk da koke-koken da aka gabatar daga wasu wakilai da shugabannin yankin Erin-Ile
- Sarkin ya ce masu zaben sarki sun bada sunan shi, amma daga baya wasu ’yan gidan sarauta suka canza masu ra’ayi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kwara - Mai martaba Elerin na kasar Erin-Ile, Adesoye Adebowale Jimoh ya bada labarin yadda ya samu sarauta.
Adesoye Adebowale Jimoh ya bada labarin yadda ya samu sarauta duk da cewa an zo canza ra’ayin masu zaben sarki.

Source: Facebook
Sarkin Erin-Ile ya fuskanci adawa wajen nada shi
Sarki Adesoye Adebowale Jimoh ya ce dattawa, sarakai da wasu ‘yan majalisa sun yi adawa da shi a cewar Daily Trust.
Duk da yadda aka nuna wa gwamnan Kwara ba a so a nada shi, haka nan Mai girma Abdulrahman AbdulRazaq ya zabe shi.
Sarkin ya yi wannan bayani ne wajen kaddamar da sabon fadar da aka gina masa a Erin-Ille a karamar hukumar Oyun.
“Lokacin da aka fara shirin nada ni a matsayin Elerin na Erin-Ile, kimanin shekaru biyu da suka wuce, an samu ce-ce-ku-ce sosai, saboda ni ba ne zabin da mutane da dama suka fi so ba.”
Yadda 'yan majalisa suka canza shawarar nada sarki
Mai martaba Adesoya Jimoh ya ce majalisar zaben sarki ta goyi bayan shi, amma wasu suka bukaci soke shirin da aka yi.
Ya ce da yake gwamna yana ganin girman masarautun gargajiya, sai ya hau kan wannan zabi da suka yi kuma ya zauna a kai.
Ya ce:
"(Gwamna) ya dage cewa ba zai soke matakin da suka (majalisar zaben sarki) dauka ba sai dai idan al’umma ta cin ma matsaya."
Sarkin ya ce a karshe jama’a sun yi na’am da shi, suka amince ya yi sarauta kuma ya nemi hadin-kan su.
Sarkin Erin-Ile ya gode wa Gwamnan Kwara
A jawabin da ya yi, Mai martaban wanda aka fi sani da Elerin a kasar Erin-Ile ya gode da goyon bayan da gwamna ya ba shi.

Kara karanta wannan
Raddin da Jalo Jalingo ya yi wa sarakuna ya sa ya ji babu daɗi hannun ƴan Facebook
"Saboda haka na sadaukar da wannan fada ga Mai girma (gwamna), domin ba don jajircewar shi ga masarautun gargajiya ba da nacewar sai an bi maganar masu zaben sarki, da ba a yi nasarar yin wannan aiki ba."
- Oba Jimoh Adebowale Adeosoye
A wata hira da The Nation, sarkin ya tabbatar da ya gaji sarauta daga wurare biyi - masarautarsa da ta Sefwi Wiawso a Ghana.
Abin da ya jawo rikicin sarauta a kasar Oyun
An samu rikici ne wajen nada sarkin da zai gaji AbdulGaniyu Ajibola Olusokun II wanda ya rasu a cikin watan Mayun 2023.
Lokacin neman sarautar, Yarima Joel Omokanye, ya kalulanci yadda aka zakulo ‘yan majalisar da ke da alhakin zaben sarki.
Sunayen Jimoh Adeoye, Rauf Usman Aroyehun da Adewale Omorinoye aka aika wa gwamna, kuma ya zabi sarki a lokacin.
A ranar 19 ga watan Oktoba 2024 gwamna ya mika sandar sarauta ga Sarki Jimoh Adebowale Adeosoye.

Source: Facebook
Lokacin da aka tsaida nadin sarki a Najeriya
Kwanakin baya aka ji labari Olubadan na Ibadan, Oba Owolabi Akinloye Olakulehin, ya dakatar da dukkan shirye-shiryen nadin sarauta a jihar.

Kara karanta wannan
Tinubu: Nasir El Rufai ya daura bidiyon abin da Sarkin Katsina ya fada wa Abdulaziz Yari
An dauki matakin ne saboda yadda wasu kungiyoyi suka shirya nadin Iyalode na Oyo ba bisa ka'ida ba.
Kwamitin masarautar ya haramta ba da sarauta ta bayan fage tare da gargadin ’yan kasuwa da su mai da hankali kan sana'ar da take gabansu.
Asali: Legit.ng
