Saura Kwana 80 Zabe, An Ji Gwamnati Tana Binciken Su Peter Obi da Shugaban ADC
- CCB tana binciken Peter Obi, Bukola Saraki, David Mark da wasu kan zargin boye dukiyoyinsu da ke kasashen waje
- Binciken ya danganta wasu daga cikinsu da mallakar kadarori da kamfanonin a Birtaniya amma suka ki bari CCB ta san da su
- An nemi jin kwa-kwaf, kuma an gano ana kan bincike. Sai dai hakan ba ya nufin an tabbatar da laifin wadanda ake zargi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Hukumar da'ar ma'aikatan gwamnati ta Najeriya (CCB) tana kan binciken wasu 'yan siyasa da tsofafin jami'an gwamnati.
Mutane akalla bakwai aka fahimci cewa ana bincike bisa zargin saba doka wajen mallakar kadarori da harkokin kasuwanci ketare.

Source: Getty Images
Rahoto na musamman daga Premium Times ya ce wadannan mutane suna harkoki a kasashen waje ba tare da sun shaida wa CCB ba.
Majiyoyi da dama a hukumar sun tabbatar da fara binciken fitattun ‘yan siyasan da kuma wasu da suka yi aikin gwamnati a kasar.
Ana binciken badakalar Panama da Pandora Papers
Mutanen da rahoton badakalar Panama Papers da Pandora Papers suka ambata sun hada da Peter Obi mai neman takara a NDC.
Akwai tsofaffin shugabannin majalisar dattawa biyu wadanda kuma sun taba zama gwamnoni a Najeriya; Bukola Saraki da David Mark.
Haka zalika Stella Oduah da taba zama minista a lokacin Goodluck Jonathan da marigayi tsohon gwamna, Diepreye Alamieyeseigha.
Cikin wadanda jami’an CCB suka taso a gaba akwai Stella Ogene, tsohuwar shugabar Kotun daukaka kara ta Gargajiya a jihar Delta.
Rahoton ya kuma tattauna binciken da ya shafi Nicholas Mutu, dan Majalisar Wakilai da ake zargi yana da kamfanonin kasashen waje.
An tasa CCB a gaba game da binciken
Cikin watan Yulin nan sai jaridar ta tuntubi CCB domin jin ina aka kwana game da wannan bincike da aka nemi a manta da shi tun 2021.
A Satumban 2026, hukumar CCB ta shaida mata tana nazarin bayanai da takardun da suka shafi zargin da ake yi wa mayan mutanen.

Kara karanta wannan
Nesa ta zo kusa: CDCFIB za ta sake bude shafin ɗaukar ma'aikata a hukumomi 4 a Najeriya
Abin da jami’an na CCB suka fada masu shi ne za su bi ka’ida wajen daukar matakin da ya dace.
Bugu da kari, hukumar ta ce idan har akwai bukata za ta nemi wani wakilin jaridar ya yi mata karin bayani yayin da ake bincike.
An ji labari cewa CCB ta ki yarda ta yi wani karin bayani, ta ce ana yin binciken ne a asirce.
CCB tana binciken Obi, Odua, Mutuh
A shekarar 2021, aka wallafa wani bincike da ya danganta Peter Obi da wasu harkokin kasuwanci a kasashen waje sa'ilin yana gwamna.
Binciken ya ce Obi ya ci gaba da zama daraktan kamfanin NEXT International (UK) Ltd baya ga mallakar asusun bankin waje lokacin.
Obi bai musanya wannan ba, sai dai ya yi hujja da jahiltar sanin doka. Sai dai dama ba a zargi ‘dan siyasar da karkatar da wasu kudi ba.
Ita kuwa Stella Oduah, ganowa aka yi ta mallaki gidaje a Landan na fam miliyan 6.7, ta hannun wani kamfanin kasar Seychelles.
An ce an sayi gidajen tsakanin Oktoba 2012 da Agusta 2013 da ta ke ministan jiragen sama.
Binciken Pandora Papers ya danganta Stella Ogene da wani kamfani da aka kafa a Seychelles (Assete Media Limited) a 2009.
An yi amfani da Assete Media Ltd wajen sayen gida a Birtaniya. Kuma an gano Ogene a matsayin mai kamfanin, darakta da sakatarensa.
Shi ma Nicholas Mutu zargin da ake yi masa shi ne kafa wani kamfani a Seychelles a shekarar 2010 alhali lokacin yana 'dan majalisae wakilai.
Kamfanin, Forest Group of Company, ya sayi wani gida a arewacin Landan kan $620,000 tun 2012, sannan aka sayar da shi $730,000.
Tsofaffin gwamnonin da ake bincike
A binciken aka gano iyalan Bukola Saraki suna da kadarori a kasasheda ba a bayyana wa CCB ba.
An gano akalla kadarori hudu da ke da alaka da matarsa, Toyin Saraki, wadanda aka rike ta hannun wasu kamfanoni a kasashen waje.
Daga cikin kamfanonin akwai Sandon Development Limited, wanda aka kafa a Seychelles kuma aka yi amfani da shi wajen sayen gida.
Akwai kamfanonin Girol Properties Limited da Landfield International Developments Limited da duk ake ganin na su Sanata Saraki ne.
Rahoton Panama Papers ya danganta David Mark da kamfanoni akalla takwas da aka yi wa rajista a da yake ofis a majalisar dattawa.
Kamfanonin sun hada da Sikera Overseas S.A., Colsan Enterprises Limited, Goldwin Transworld Limited da Hartland Estates Limited.
Rahoton ya ce marigayi Diepreye Alamieyeseigha ya yi amfani da kamfanonin kasashen waje wajen rike kadarori da tura kudi zuwa waje.
Tsohon gwamnan Bayelsa ya yi amfani da kamfanin Solomon & Peters Limited, wanda aka kafa a wani tsibirin kasar waje tun 1999.
Binciken ya danganta shi da kadarori a Birtaniya, Amurka da Afrika ta Kudu, da asusun bankunan kasashen waje da ba a san da su ba.
Wani tsohon gwamnan shi ne James Ibori wanda ya yi mulki daga 1999 zuwa 2007. An gano yana harkar kasuwanci a waje a sirrance.

Source: Getty Images
Shari'ar ICPC da El-Rufai a kotu
Idan aka dawo gida, an ji labari kotu ta amince da bukatar ICPC na nuna faifan CCTV a shari’ar N10bn da Nasir El-Rufai ya shigar.
Tsohon gwamnan ya nemi diyya saboda zargin hana shi ganawa da matarsa da ɗansa da yake tsare bayan ya mikan kan gaban hukuma.
Alƙali Chigozie Onah ɗage sauraron ƙarar El-Rufai da ICPC zuwa 3 ga Nuwamba, 2026 kuma ya amince da bukatun lauyan gwamnati.
Asali: Legit.ng


