Lokaci Ya Yi: Dattijon Kasa kuma Jagoran Kungiyar Afenifere ta Najeriya Ya Rasu
- Pa Reuben Famuyide Fasoranti, dattijon ƙasa kuma jagoran ƙungiyar Afenifere mai fafutukar kare al'adun Yarabawa, ya rasu yana da shekaru 100
- Gwamnan Jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa, ne ya sanar da rasuwarsa a ranar Talata a wata sanarwa da ya sanya wa hannu da kansa a Akure
- Gwamnan ya bayyana marigayin a matsayin dattijo mai hikima, gaskiya da sadaukar da kai wajen yi wa Jihar Ondo, ƙasar Yarabawa da Najeriya hidima
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ondo, Nigeria - Dattijon ƙasa kuma jagoran ƙungiyar Afenifere mai fafutukar kare al'adu, zamantakewa da siyasa ta Yarabawa, Pa Reuben Famuyide Fasoranti, ya rasu yana da shekaru 100 a duniya.
Gwamnan Jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa, ne ya sanar da rasuwar marigayin a ranar Talata, 20 ga watan Oktoban 2027.

Source: Facebook
Gwamna ya sanar da rasuwar Fasoranti
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa gwamnan ya tabbatar da rasuwar dattijon ne a cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu da kansa a Akure, babban birnin jihar Ondo.
Gwamnan ya bayyana Fasoranti a matsayin dattijon ƙasa mai daraja, wanda rayuwarsa ta kasance cike da hikima, gaskiya da sadaukar da kai wajen yi wa Jihar Ondo, ƙasar Yarabawa da Najeriya hidima.
Haka zalika, Aiyedatiwa ya ayyana marigayi Pa Fasoranti a matsayin wanda ya kasance uban al’umma kuma abin koyi wajen hikima, gaskiya da hidima ba tare da son kai ba.
Gwamnan Ondo ya fadi alherin marigayin
A sanarwar, Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya ce:
“Cikin baƙin ciki, amma tare da miƙa wuya ga ikon Ubangiji, ina sanar da rasuwar dattijonmu mai daraja, Pa Reuben Famuyide Fasoranti, wanda ya bar duniya yana da shekaru 100 masu albarka.
“Pa Fasoranti ya kasance uban al’umma kuma abin koyi wajen hikima, gaskiya da hidima ba tare da son kai ba. Rayuwarsa ta tsawon ƙarni guda ta kasance cike da jajircewa ta musamman wajen bunƙasa jiharmu mai albarka, ƙasar Yarabawa da Najeriya baki ɗaya.
“Shawarwarinsa, jagorancinsa na uba da kuma tsayin daka da ya saba yi kan batutuwan adalci da shugabanci nagari za a yi matuƙar kewar su. Ya rayu rayuwa mai cike da gamsuwa, kuma ya bar tarihi mai ɗorewa na mutunci da kyakkyawan abin tunawa ga tsararraki masu zuwa.”
Aiyedatiwa ya mika sakon ta'aziyya
A madadin Gwamnatin Jihar Ondo da al’ummarta, Gwamna Aiyedatiwa ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan Fasoranti, al’ummar masarautar Akure da kuma daukacin jihar.
Ya kuma yi addu’ar Allah Ya jiƙan mamacin, yana mai cewa: “Allah Ya sa ruhinsa mai tawali’u ya huta cikin cikakkiyar salama.”
Karin bayani na nan tafe...
Asali: Legit.ng

