'Yan Bindiga Sun Farmaki Ayarin Motoci a Sokoto, an Kashe Malami da Sauran Mutane
- An kashe sabon malamin makaranta, Maniru Sa’adu Imam, mai shekara 30, tare da wasu mutum biyu a harin ’yan bindiga a Sokoto
- Marigayin ya je birnin Sokoto ne domin tantance bayanansa gabanin fara biyan albashinsa na farko
- An kashe direban motar, Abdurrahman Umar, da ɗansa mai shekara biyar, yayin da wasu mutum uku suka jikkata, mutum ɗaya kuma ya ɓace
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Sokoto - Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kashe wani sabon malamin makaranta a Jihar Sokoto, Maniru Sa’adu Imam.
'Yan bindigan sun kashe shi ne sa’o’i kaɗan bayan ya halarci aikin tantance bayanan ma’aikata domin fara karɓar albashi a cikin birnin Sokoto.

Source: Original
Rahoton jaridar Daily Trust ya nuna cewa an kashe Imam, mai shekara 30 kuma mahaifin yaro ɗaya, tare da wasu mutum biyu a ranar Laraba, 21 ga watan Oktoban 2026.

Kara karanta wannan
Abin da cutar Ebola ke yi a jikin dan adam, da yadda za ku kare kan ku daga kamuwa
Malamin ya rasa ransa ne lokacin da ’yan bindigar suka yi wa motocin da ke tafiya a kan hanyar Gundumi zuwa Isa kwanton ɓauna.
Sauran waɗanda aka kashe sun haɗa da Abdurrahman Umar, direban motar da ke ɗauke da su, da ɗansa mai shekara biyar, Abubakar Abdurrahman.
Yadda 'yan bindiga suka kai harin
Wani ganau, Malam Kabiru Isa, ya bayyana cewa waɗanda abin ya shafa suna tafiya ne a bayan ayarin motocin da ke komawa garin Isa, tare da rakiyar jami’an tsaro masu ɗauke da makamai.
Ya ce saboda matsalar tsaro a yankin, mazauna Isa kan je birnin Sokoto sau biyu kacal a mako, wato ranar Laraba da Asabar.
A cewarsa, ayarin motocin ya bar wurin da misalin ƙarfe 4:00 na yamma a ranar Laraba, amma wasu motocin, ciki har da wadda ke ɗauke da waɗanda aka kashe, sun koma wurin da suka saba haɗuwa bayan sauran motocin sun tafi.
“Mun so mu jira duk mutanen da suka yi tafiya tare da mu, amma jami’an tsaro suka dage cewa mu tashi da wuri, don haka muka bar su a baya.” In ji shi.
Jami'an tsaro sun yi rakiya
Isa ya bayyana cewa yayin da ayarin motocin ke gabatowa Gundumi, jami’an tsaron da ke yi musu rakiya sun hangi wasu mutanen da ake zargin ’yan bindiga ne, sannan suka buɗe musu wuta, lamarin da ya tilasta musu tserewa.
Sai dai ya ce daga baya maharan sun yi wa motocin da ke biye da ayarin kwanton ɓauna, inda suka buɗe wa fasinjojin wuta.
“Sun kashe mutum uku, ciki har da Imam, direban da ɗansa. Sun kuma jikkata wasu mutum uku, yayin da fasinja ɗaya har yanzu ba a san inda yake ba.” In ji shi
Marigayin bai karɓi albashinsa na farko ba
Malam Kabiru Isa ya bayyana cewa Maniru Sa’adu Imam na cikin malaman da Gwamnatin Jihar Sakkwato ta ɗauka aiki kwanan nan, inda aka tura shi zuwa Makarantar Sakandaren Gwamnati da ke Maitandu.
Ya ce marigayin bai fara karɓar albashinsa ba, shi ya sa ya yi tafiya zuwa birnin Sokoto a ranar Laraba domin tantance bayanansa kafin a fara biyan albashinsa.
A cewar Malam Kabiru Isa, an binne waɗanda aka kashe a safiyar ranar Alhamis, 22 ga watan Oktoban 2026.
A halin da ake ciki, ƙoƙarin samun tabbaci daga rundunar ’yan sandan Jihar Sokoto bai yi nasara ba, domin kakakinta, DSP Ahmad Rufa’i, bai amsa kiran wayar da aka yi masa ba.
Saboda haka, har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, rundunar ’yan sandan ba ta tabbatar da faruwar lamarin a hukumance ba.

Source: Facebook
'Yan sanda sun cafke dan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar ƴan sandan jihar Sokoto ta kama wani mutum da ake zargi da kasancewa ɗan bindiga da hannu a satar dabbobi.
An kama wanda ake zargin ne a wata kasuwa, inda aka same shi dauke da wata akuya da daga bisani mai ita ya gane cewa tana cikin dabbobin da aka sace.
Asali: Legit.ng

