An Gargaɗi Jami'an Tsaro kan Harbin Jama'a bayan Yi wa Tinubu Ihu a Masallaci
- Tsohon Ministan Matasa da Wasanni, Solomon Dalung, ya gargadi jami’an tsaron Shugaba Tinubu kan amfani da bindiga wajen murkushe masu zanga-zanga
- Dalung ya ce babu wani dalili da zai halatta harbin ’yan Najeriya saboda nuna fushinsu kan gwamnatin da suke ganin ta gaza
- Ya yi gargadin cewa bude wuta kan masu zanga-zanga na iya haddasa mummunan rikici tare da jefa gwamnati cikin babbar matsala
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Tsohon Ministan Matasa da Wasanni, Solomon Dalung, ya gargadi jami’an tsaron Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan yiwuwar amfani da bindiga wajen harbe ’yan Najeriya da ke gudanar da zanga-zanga.
Dalung ya bayyana cewa babu wata gwamnati da za ta iya amfani da makamai wajen dakile fushin al’umma, yana mai cewa hakan na iya haifar da mummunan sakamako.

Source: Facebook
Ya yi wannan gargadin ne bayan ce-ce-ku-cen da ya biyo bayan wani bidiyo da aka yada a Facebook, inda wasu matasa sun jefe ayarin motocin Shugaba Tinubu bayan ya ziyarci wani masallaci a Abuja.
Abin da ya faru bayan ziyarar Tinubu masallaci
Lamarin ya faru ne ranar Juma’a bayan Shugaba Tinubu ya halarci sallar Juma’a a babban masallacin Shehu Shagari da ke babban birnin tarayya Abuja.
Wasu bidiyoyi da suka karade kafafen sada zumunta sun nuna wasu matasa suna rera kalaman kin amincewa da shugaban kasar tare da jifan wasu abubuwa zuwa ayarin motocin da ke barin masallacin.
Sai dai fadar shugaban kasa ta musanta rahotannin cewa an kai wa ayarin motocin Tinubu hari.
Mai taimaka wa shugaban kasa, O’tega Ogra, ya fitar da wani bidiyo na daban, inda ya ce an ga shugaban kasar yana barin masallacin cikin farin ciki da murnar magoya bayansa.

Source: Getty Images
Dalung ya yi gargadi kan amfani da bindiga
Da yake martani kan lamarin, Dalung ya bukaci masu goyon bayan amfani da karfin makami wajen murkushe masu zanga-zanga da su yi la’akari da illar hakan.
Ya ce jami’an tsaron shugaban kasa ba sa fuskantar wata rundunar soji ko ’yan ta’adda masu dauke da makamai, illa dai ’yan kasa da ke bayyana fushinsu da rashin gamsuwa da yadda ake tafiyar da gwamnati.
Tsohon ministan ya amince cewa akwai yiwuwar wasu daga cikin masu zanga-zangar sun aikata abubuwan da ba su dace ba, amma ya ce hakan bai zama hujjar harbe su ba.
Ya bayyana bude wuta kan masu zanga-zanga a matsayin wani mataki mai muni da ba za a iya yafe wa ba, wanda zai iya mayar da karamin rikici zuwa babbar matsalar kasa.
Dalung ya nuna fargaba kan zaben 2027
An ji cewa tsohon Ministan Matasa da Wasanni, Solomon Dalung, ya zargi sakataren ADC na ƙasa, Rauf Aregbesola, da naɗa kwamitocin riƙon ƙwarya a jihohi.
Dalung ya ce naɗin ya zo ne yayin da ake jiran hukuncin Kotun Ƙoli kan takaddamar shugabancin jam’iyyar.
Ya bukaci ADC ta dakatar da rantsar da kwamitocin da aka shirya yi domin kada hakan ya jefa shigar jam’iyyar zaɓen 2027 cikin haɗari.
Asali: Legit.ng

