Ana Shirin Zaben 2027, Gwamna Radda Ya Runtuma Kora a Gwamnatinsa
- Gwamna Dikko Radda ya amince da sallamar Babban Manajan KTTV, Malam Abba Zayyan, nan take
- Gwamnatin Katsina ta ce ta kashe makudan kuɗaɗe wajen sayen kayan aiki da inganta kayayyakin more rayuwa na tashar
- An umarci babban jami’in da ya fi kowa matsayi a KTTV ya jagoranci tashar a matsayin mukaddashin manaja har sai an naɗa sabon shugaba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Katsina - Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya amince da sallamar Babban Manajan gidan talabijin na jihar, Katsina State Television (KTTV), Malam Abba Zayyan, nan take.
Gwamnan ya ɗauki matakin ne bisa zargin cewa manajan ya kasa tafiyar da tashar yadda ya dace da manufofin gwamnatinsa, duk da makudan kuɗaɗen da aka zuba wajen inganta ayyukanta.

Source: Facebook
An bayyana matakin ne a ranar Talata, 10 ga watan Nuwamban 2026 cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Yaɗa Labaran Gwamna Radda, Ibrahim Mohammed, ya sanya a shafinsa na Facebook.
Dalilin sallamar babban manajan
Sanarwar ta ce gwamnatin jihar ta zuba makudan kuɗaɗe wajen sake fasalin KTTV domin ta kai matsayin da ake buƙata a harkokin watsa shirye-shirye na ƙasa da ƙasa.
Ta bayyana cewa gwamnati ta samar da na’urorin zamani, ta inganta muhimman kayayyakin more rayuwa tare da ba tashar cikakken goyon bayan hukumomi.
Manufar waɗannan matakai ita ce mayar da KTTV wata kafar watsa shirye-shirye mai ƙwarewa, inganci da gasa, wadda za ta iya tallata kyakkyawan hoton Jihar Katsina.
Sai dai Gwamna Radda ya nuna rashin jin daɗinsa kan yadda tashar ta ci gaba da gudanar da ayyukanta ƙasa da matakin da ake tsammani, duk da irin tallafin da aka ba ta.
A cewar sanarwar, tashar ta gaza isar da manufofi, shirye-shirye da nasarorin gwamnatin jihar ga al’ummar Katsina da sauran masu sauraro yadda ya kamata.
Gwamna Radda ya jaddada ingantaccen aiki
Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatinsa na da ƙudirin tabbatar da cewa kowace cibiyar gwamnati tana gudanar da ayyukanta yadda ya kamata.
Ya ce dole ne dukkan hukumomin gwamnati su yi aiki bisa hangen nesan gwamnatinsa, wanda ya haɗa da gaskiya, riƙon amana da samar da ayyuka masu inganci.
A cewarsa, wannan ƙudiri ne ya sa yake buƙatar kowace hukuma ta yi amfani da albarkatun da aka ba ta wajen cimma manufofin da aka kafa ta dominsu.
An naɗa mukaddashin shugaban KTTV
Domin tabbatar da cewa ayyukan KTTV ba su tsaya ba sakamakon sallamar babban manajan, Gwamna Radda ya umarci babban jami’in da ya fi kowa matsayi a tashar ya karɓi ragamar jagorancinta na riƙon ƙwarya.
Sanarwar ta ce zai ci gaba da gudanar da ayyukan tashar a matsayin mukaddashin babban manaja har sai an naɗa wanda zai riƙe muƙamin na dindindin.
A ƙarshe, Gwamna Radda ya nuna godiyarsa ga Malam Abba Zayyan bisa hidimar da ya yi wa jihar a lokacin da yake jagorantar tashar. Ya kuma yi masa fatan samun nasara a sauran al’amuransa na gaba.

Source: Facebook
Gwamna Radda ya magantu kan rashin tsaro
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya sake tabbatar da aniyarsa ta kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro a ƙaramar hukumar Matazu.
Gwamna Radda ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta ƙarfafa haɗin gwiwa da jami'an tsaro, sarakunan gargajiya da shugabannin al'umma domin kare rayuka da dukiyoyin jama'a.
Asali: Legit.ng

