Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Nemi Aron Aso Rock domin Kaddamar da Kamfen

Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Nemi Aron Aso Rock domin Kaddamar da Kamfen

  • Jam’iyyar AAC ta Omoyele Sowore ta tura bukata ta musamman ga Shugaba Bola Tinubu ya ba ta izinin ƙaddamar da kwamitin kamfen
  • Jam’iyyar ta kuma nemi a samar da abinci, abubuwan sha da sauran kayan tallafi ga mahalarta taron da aka tsara gudanarwa
  • AAC ta ce amincewa da buƙatarta za ta nuna adalci, daidaito da kuma bai wa dukkan jam’iyyun siyasa damar amfani da cibiyoyin gwamnati

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Jam’iyyar African Action Congress (AAC) da Omoyele Sowore ke neman takara ta tura bukata ga Bola Tinubu.

AAC ta nemi Shugaba Bola Tinubu ya amince ta yi amfani da fadar shugaban ƙasa da ke Abuja domin ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasarta.

Sowore ya tura babbar bukata ga Tinubu
Shugaba Bola Tinubu da Omoyele Sowore. Hoto: Bayo Onanuga, Omoyele Sowore.
Source: Twitter

A cikin wasiƙar da Vanguard ta samu, jam’iyyar ta bayyana cewa taron wani ɓangare ne na shirye-shiryenta na babban zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

"Babu zagi": Yari ya fadi abin da za su tallata Shugaba Tinubu da shi

Sauran bukatun AAC ga Tinubu

Jam’iyyar ta kuma nemi a samar da abinci, abubuwan sha da sauran tallafin kayan aiki ga mahalarta taron da aka shirya gudanarwa ranar 11 ga Nuwamba, 2026.

AAC ta gabatar da buƙatun ne a cikin wata wasiƙa mai kwanan watan 21 ga Oktoba, 2026, wadda ta aika wa shugaban ƙasa, kuma sakataren jam’iyyar na ƙasa, Oshiokhai Ikpeminioghena, ya sanya wa hannu.

Wasiƙar ta ce:

“A madadin jam’iyyar African Action Congress (AAC), ina rubuto wannan wasiƙa cikin girmamawa domin neman izinin gudanar da bikin ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasarmu a ranar 11 ga Nuwamba, 2026, a fadar shugaban ƙasa da ke Aso Rock, Abuja, a shirye-shiryen babban zaɓen shekarar 2027.”
Sowore ya nemi aron Aso Rock domin kamfen
Dan takarar shugaban kasa a AAC, Omoyele Sowore. Hoto: Omoyele Sowore.
Source: Facebook

Musabbabin tura bukatun da AAC ta yi

Jam’iyyar ta ce buƙatarta ta samo asali ne daga ƙa’idojin dimokuraɗiyyar jam’iyyu da dama, haɗa kowa cikin harkokin siyasa da kuma yi wa dukkan jam’iyyun siyasa adalci.

Kara karanta wannan

'Farashin abinci ya zube kasa warwas a Najeriya saboda tsare tsaren Tinubu'

AAC ta yi jayayya cewa amincewa da buƙatarta zai nuna cewa fadar shugaban ƙasa ta himmatu wajen tabbatar da adalci da daidaiton damar amfani da cibiyoyin gwamnati.

Ta bayyana a cikin wasiƙar cewa:

“Domin tabbatar da dimokuraɗiyyar jam’iyyu da dama, haɗa kowa cikin harkokin siyasa da yi wa jam’iyyun siyasa daidai, muna kuma neman a samar da abinci, abubuwan sha da sauran tallafin kayan aiki ga mahalarta taron, kamar yadda aka bayar da irin wannan tallafi ga jam’iyyar APC a wani taron siyasa makamancin haka."

Jam’iyyar ta ce tana fatan samun amsa mai kyau, tare da neman a sanar da ita hanyoyin da za a bi da kuma sharuɗɗan da ake buƙata domin amincewa da buƙatar.

An zargi da yi wa Atiku aiki

An ji cewa dan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar AAC, Omoyele Sowore, ya zargi Peter Obi da goyon bayan Atiku Abubakar.

Sowore ya yi zargin ne a wani saƙo da ya wallafa, inda ya ce Obi na adawa da manufofinsa na kawo sauyi a Najeriya.

Zargin ya jawo martani daga masu amfani da kafafen sada zumunta, inda wasu suka goyi bayan Sowore, wasu suka kare Obi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.