Kungiyar SERAP ta roki a hana ‘Yan siyasa da masu iko kashe kudi kan motoci
- SERAP ta ce Buhari ya sa hannu a dokar da za ta hana Ministocinsa sayen motoci
- ‘Yan siyasar kasar nan sun saba kashe kudi wajen sayen manyan motoci bini-bini
- Kungiyar ta na so Shugaban Najeriya ya yi koyi da Takwaransa na kasar Namibiya
Kungiyar SERAP mai bin diddikin ayyuka da kare hakkin mutanen Najeriya ta yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ya hana ‘yan siyasar kasar sayen sababbin motoci.
SERAP ta bukaci a haramtawa duk wani ‘dan siyasa kamar wadanda ke rike da kujerar minista a gwamnatin tarayya sayen mota har zuwa lokacin da wa’adin shugaban kasar zai cika.
Wannan kungiya ta yi kiran nan ne a wata wasika da ta aikawa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, inda ta nemi ya yi koyi da kasar Namibiya da ta dauki irin wannan matakin.
Kungiyar ta SERAP ta ce: “Shugaban kasa ya rattaba hannu kan dokar da za ta hana ma’aikatan fadar shugaban kasa da duk ministocinsa canza motoci har ya sauka daga mulki.”
KU KARANTA: Abin da ya sa Majaliar Najeriya za ta kashe Biliyoyi a kan motoci
Idan har aka iya yin haka, za ayi amfani da kudin da aka adana wajen yaki da annobar cutar COVID-19. Wa’adin shugaban na Najeriya zai kare ne a karshen watan Mayu 2023.
Wannan kungiya mai kare hakkin mutanen Najeriya ta yi kira ga shugaba Buhari ya nemi ‘yan majalisar tarayya da gwamnonin jihohi su daina sayen wasu sababbin motocin hawa.
SERAP ta na so ayi amfani da wannan kudi wajen biyan ma’aikata da ‘yan fansho. Jaridar Punch ta ce matakin da shugaba Hage Geingobon zai adanawa Namibiya fam Dala miliyan 10.
Bayan haramta sayen motoci, SERAP ta na so a dakatar da kashe kudi wajen sayen injin wuta, kayan tebura da kujeru da duk wasu kayan kyale-kyale a ofisoshi da gidajen manya.
“Koyi da Namibiya zai sa a rika kashe dukiyar kasa wajen amfanin jama’a, a maimakon manyan ‘yan siyasa kadai su rika cin moriyar gwamnati.” SERAP ta rubuta a wasikarta ta.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng