Takarar Gwarzo: Ƴan Kwankwasiyya Sun Yi Zanga Zanga a Ofishin INEC na Kano

Takarar Gwarzo: Ƴan Kwankwasiyya Sun Yi Zanga Zanga a Ofishin INEC na Kano

  • Magoya bayan Kwankwasiyya sun gudanar da zanga-zangar lumana a Kano, suna neman INEC ta dawo da sunan ɗan takarar gwamnan NDC
  • Mataimakin ɗan takarar mataimakin gwamna na NDC, Mustapha Rabiu Kwankwaso ne ya jagoranci masu zanga-zangar zuwa ofishin INEC
  • Kwankwasiyya ta zargi wani ma’aikacin INEC da hannu wajen amfani da takardun da ake zargin an ƙirƙira sa hannun bogi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Magoya bayan tafiyar Kwankwasiyya sun gudanar da zanga-zangar lumana a Kano ranar Juma’a bayan INEC ta fitar sunayen yan takara.

Yan Kwankwasiyyar sun gudanar da zanga-zangar lumana a Kano, suna neman INEC ta dawo da sunan ɗan takarar gwamnan NDC, Aminu Abdussalam Gwarzo, cikin jerin sunayen ’yan takara.

Yan Kwankwasiyya sun yi zanga-zanga a Kano
Dandazon yan Kwankwasiyya yayin zanga-zanga a Kano. Hoto: Kwankwasiyya Reporters.
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa sunan Gwarzo bai bayyana cikin jerin sunayen da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta fitar a farkon makon nan ba.

Kara karanta wannan

'Nadamar da APC za ta yi a ranar zabe': Kwankwaso ya jaddada kwarin guiwarsu

Yaron Kwankwaso ya jagoranci zanga-zanga

Mataimakin ɗan takarar mataimakin gwamna na NDC, Mustapha Rabiu Kwankwaso, ya jagoranci masu zanga-zangar zuwa ofishin INEC, inda suka miƙa takardar ƙorafi kan cire sunan Gwarzo.

Kwankwasiyya ta zargi wani ma’aikacin INEC da hannu wajen amfani da takardun da ake zargin an ƙirƙira sa hannun bogi, yayin da hukumar ta tabbatar da samun ƙorafin.

Mataimakin ɗan takarar mataimakin gwamna na jam’iyyar, Mustapha Rabiu Kwankwaso, ne ya jagoranci masu zanga-zangar zuwa ofishin INEC na jihar Kano, inda suka miƙa takardar ƙorafi.

Kwankwaso ya dage cewa jam’iyyar ta bi duk ƙa’idojin da suka shafi tsayar da ’yan takara, yana mai bayyana cire sunan Gwarzo a matsayin rashin adalci.

Kwamishinan Zaɓe na INEC a Kano, Abdu Zango, ya tabbatar da karɓar takardar ƙorafin, yana mai cewa an riga an sanar da dalilan cire sunan.

Sai dai ya tabbatar musu cewa har yanzu akwai damar ɗaukaka ƙara, inda wa’adin yin hakan zai ƙare ranar 24 ga Oktoba.

Kara karanta wannan

A karshe, Kwankwaso ya yi magana kan cire sunan Aminu Gwarzo da INEC ta yi

Ya jaddada cewa ofishin INEC na Kano ba ya goyon bayan kowace jam’iyya, sannan ya yaba wa masu zanga-zangar bisa nuna ladabi da bin doka.

Zango ya ce:

“Mun karɓi dukkan ƙorafe-ƙorafen, kuma mun tabbatar wa tawagar cewa za a ba da kulawar da ta dace ga takardar ƙorafinsu.”

Ya ƙara da cewa za su aika da takardar zuwa hedikwatar hukumar ta ƙasa domin nazari, yana mai yabawa ƙungiyar bisa gudanar da zanga-zangar cikin lumana.

Baya ga cire sunan Gwarzo, tafiyar Kwankwasiyya ta zargi wani ma’aikacin INEC da hannu wajen ƙirƙirar takardu da haɗa baki da wasu mutane.

Mai magana da yawun ƙungiyar, Dr. Habib Mohammed, ya ce an miƙa wasu wasiƙu ba tare da izini ba, waɗanda ake zargin an ƙirƙira sa hannun bogi a kansu.

A cewarsa, an kai waɗannan wasiƙu hedikwatar INEC, lamarin da ya jawo sauya sunayen wasu ’yan takara.

Ya buƙaci hukumar ta gudanar da bincike domin gano ma’aikacin da ake zargi da hannu a lamarin, tare da ɗaukar matakin da ya dace.

Dr. Mohammed ya ce: “Alhamdulillah, Kwamishinan Zaɓe ya karɓe mu hannu biyu-biyu, kuma ya tabbatar mana cewa zai tura takardar ƙorafin zuwa hedikwatar hukumar yau.”

Kara karanta wannan

Kungiyar Musulunci ta shiga batun cire sunan Pantami, ta yi kira ga Tinubu

Ƙarin bayani na tafe....

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.