Bayan Arangama Tsakanin Jam’iyyu, an Sanar da Sakamakon Zaben Ciyamomi a Kogi

Bayan Arangama Tsakanin Jam’iyyu, an Sanar da Sakamakon Zaben Ciyamomi a Kogi

  • Jam’iyyar APC ta lashe dukkan kujerun shugabannin ƙananan hukumomi 21 da kuma kujerun kansiloli 239 a zaɓen ƙananan hukumomin Jihar Kogi
  • Shugaban hukumar zaɓen jihar, Mamman Eri, ya sanar da sakamakon a Lokoja, inda ya yaba wa jami’an tsaro, masu sa ido da sauran masu ruwa da tsaki
  • Ƙungiyoyin fararen hula sun yaba da zaman lafiyar zaɓen, amma sun buƙaci wayar da kan masu zaɓe da ƙarin gaskiya domin ƙarfafa amincewar jama’a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Lokoja, Kogi - Hukumar zabe a jihar Kogi ta sanar da sakamakon zaben kananan hukumomi da aka gudanar a jiya Asabar.

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta lashe dukkan kujerun shugabannin ƙananan hukumomi 21 da kuma kujerun kansiloli 239 a zaɓen da aka yi.

APC ta lashe zaben kananan hukumomi a Kogi
Gwamna Ahmed Usman Ododo na jihar Kogi a Arewacin Najeriya. Hoto: Alhaji Ahmed Usman Ododo.
Source: Facebook

Kananan hukumomi: An kammala zabe a Kogi

Kara karanta wannan

An hura wa Tinubu wuta kan 2027, ana so ya hakura da shiga takara

Shugaban Hukumar Zaɓen Ƙananan Hukumomin Jihar Kogi (KOSIEC), Mamman Eri, ne ya sanar da sakamakon a hedikwatar hukumar da ke Lokoja, cewar Leadership.

Eri ya bayyana jam’iyyar APC mai mulki a matsayin wadda ta lashe dukkan kujerun da aka fafata a kansu.

An gudanar da zaɓen ne a mazabu 239 da rumfunan zaɓe 3,508 a faɗin jihar, duk da cewa yawan masu kaɗa ƙuri’a ya bambanta a wurare daban-daban da gidan talabijin na TVC News ya ziyarta.

Eri ya yaba wa jami’an tsaro, masu sa ido kan zaɓe, ma’aikatan wucin gadi da sauran masu ruwa da tsaki bisa yadda suka gudanar da ayyukansu yayin zaɓen.

Ya ce hukumar zaɓen ta ci gaba da jajircewa wajen gudanar da zaɓuka da suka dace da ƙa’idojin dimokuraɗiyya domin ci gaba a jihar Kogi.

An yi zaben kananan hukumomi a Kogi
Taswirar jihar Kogi da aka yi zaben kananan hukumomi. Hoto: Legit.
Source: Original

Martanin kungiyoyin fararen hula kan zaɓen Kogi

A wani ɓangaren kuma, ƙungiyoyin fararen hula sun yaba da zaman lafiyar da aka gudanar da zaɓen ba tare da samum hatsaniya ba.

Sai dai sun yi kira da a ƙara wayar da kan masu zaɓe da tabbatar da gaskiya da buɗaɗɗiyar hanya domin ƙarfafa amincewar jama’a ga tsarin zaɓe.

Kara karanta wannan

EFCC ta cafke dan babban Shehin Darika a Najeriya kan badakalar kudi

Ƙungiyoyin sun kuma buƙaci KOSIEC ta magance matsalolin da suka taso daga zaɓukan da aka gudanar a baya.

Har ila yau kungiyoyin sun bukaci daukar matakan inganta amincewar jama’a a zaɓukan da za a gudanar nan gaba domin samun jagoranci na gari.

Yobe: An sanar da sakamakon zaben ciyamomi

Mun ba ku labarin cewa jam’iyyar APC mai mulki ta lashe dukkan kujerun shugabannin ƙananan hukumomi 17 da aka fafata a zaben ranar Asabar da ta gabata a jihar Yobe.

Hukumar zabe ta YSIEC ta ce an gudanar da zaben cikin nasara a mazabu 178 da ƙananan hukumomi 17 na jihar.

Jam’iyyun adawa na APP da ADP sun samu kujerun kansiloli guda ɗaya kowannensu a Fune da Karasuwa wanda ya ba wasu mutane mamaki duba da ƙarfi APC a faɗin jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.