Wata Sabuwa: INEC na Shirin Kwace wa Shugaban Kasa Ikon Nada Kwamishinonin Zabe

Wata Sabuwa: INEC na Shirin Kwace wa Shugaban Kasa Ikon Nada Kwamishinonin Zabe

Abuja - Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta ce tana ƙoƙarin shawo kan dukkanin matsalolin da suke hana gudanar da sahihin zaɓe kafin 2027.

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ɗaya daga cikin matakan da INEC ta ɗauka shi ne neman a gyara tsarin zaɓe na ƙasa domin cire wa shugaban kasa ikon naɗa kwamishinonin zaɓe na jihohi (RECs).

Prof. Mohammad Kuna, mai ba shugaban INEC shawara na musamman, ya bayyana haka a wani taro da kwamitin majalisar tarayya kan harkokin zaɓe a Legas, inji rahoton Daily Trust.

A cewar Mohammad Kuna, sabon tsarin da ake shirin gabatarwa zai ba INEC ikon naɗa sababbin shugabannin da za a kira "daraktocin zaɓe na jihohi" maimakon RECs.

Hukumar na kuma neman canza katin zaɓe daga PVC zuwa katin da za a iya amfani da shi a manhajar intanet domin sauƙaƙa wa masu kada ƙuri'a.

INEC na neman a gyara Sashe na 14 (3) sakin layi na F a jadawalin na uku na kundin tsarin mulki don ba ta damar naɗawa da ladabtar da shugabannin ofisoshinta a jihohi da Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka kuma, hukumar na son a gyara Sashe na 6 (3) na dokar zaɓe ta 2022 domin tabbatar mata da ikon naɗa shugabannin jihohi da Abuja.

Mohammad Kuna ya ce waɗannan shugabanni za a fi saninsu da suna daraktocin zaɓe na jihohi (SDEs), kuma wannan mataki zai ƙarfafa gaskiya da inganci a tsarin zaɓe.

Yanzu haka dai, REC ne ke jagorantar ayyukan INEC a kowace jiha kuma yana jagorantar zaɓukan shugaban ƙasa, na majalisa, gwamna da na 'yan majalisar jiha.

REC na aiki ne bisa ikon da shugaban INEC da kwamishinoni 12 suka ba shi, tare da jagorantar shirye-shirye da tabbatar da ingancin sakamakon zaɓe.

Yanzu haka, bisa Sashe na 154 (1) na kundin tsarin mulki, ikon naɗa REC yana hannun shugaban kasa, amma INEC na son a sauya wannan doka.

Sabon shirin zai bai wa INEC ikon ladabtar da REC ɗin da suka karya doka kamar na jihar Adamawa da ya bayyana sakamakon da bai da hurumi akai.

INEC na kuma son a gyara wasu sassa na kundin tsarin mulki domin samar da damar kada ƙuri’a ta musamman ga ‘yan fursuna da ‘yan Najeriya da ke a ƙetare.

Haka kuma, hukumar na neman a kafa sabuwar Hukumar Laifukan Zaɓe da wata Hukumar Kula da Jam’iyyu domin tsabtace harkokin siyasa a ƙasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.