Majalisar Dattawa Ta Amince da Buƙatar Tinubu, An Kori Kwamishinoni 3 daga Aikin INEC

Majalisar Dattawa Ta Amince da Buƙatar Tinubu, An Kori Kwamishinoni 3 daga Aikin INEC

  • Majalisar dattawa ta amince da bukatar shugaba Bola Tinubu na tsige kwamishinonin hukumar zaɓe ta ƙasa watau REC na jihohi uku
  • Hudu Ari, kwamishinan zaɓen Adamawa wanda ya ayyana Aishatu Binani a matsayin wacce ta samu nasara na cikin waɗanda aka kora
  • Shugaban ƙasa ya nemi korar kwamishinonin hukumar ta INEC ne sakamakon laifuffukan da suka aikata tun a lokacin babban zaɓen 2023

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Majalisar Dattawa ta amince da buƙatar Bola Ahmed Ahmed Tinubu na tsige kwamishinonin hukumar zaɓe ƙasa watau RECs na jihohi uku a Najeriya

A zaman ranar Laraba, 5 ga watan Fabrairu, 2025, Majalisar Dattawa ta amince Tinubu ya kori kwamishinonin INEC na jihohin Sakkwato, Abia, da Adamawa.

Majalisar Dattawa.
Majalisar Dattawa ta amince Shugaba Tinubu ya kori kwamishinonin zabe na jihohi 3 Hoto: Nigeria Senate
Asali: Facebook

Sanatocin sun yanke wannan shawara ne bayan nazarin wasiƙar da shugaban ƙasar ya aika, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gwamna ya gano badaƙalar kudi, ya dakatar da kwamishina da shugaban hukuma nan take

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya kori kwamishinonin INEC 3

A wasiƙar, Bola Tinubu ya nemi a tsige kwamishinonin zaɓe uku da suka kunshi Dr. Nura Ali (Sokoto), Hudu Yunusa Ari (Adamawa) da Farfesa Ikemefuna Chijioke Uzochukwu (Abia).

Wadannan kwamishinonin zaɓen watau REC an dakatar da su daga aiki tun a shekarar 2023 saboda zarge-zargen da suka shafi aikinsu na zaɓe.

A yayin zaman majalisar, Shugaban Masu Rinjaye, Sanata Opeyemi Bamidele, ya gabatar da ƙuduri kan wannan batu na korar kwamishinonin zaɓe uku.

Laifuffukun da kwamishinonin zaɓen suka aikata

Ya bayyana cewa:

"Bisa ga rahotannin hukumomin tsaro, Dr. Nura Ali an same shi da laifin yin almundahana a zaɓen 2023, inda ya amsa karɓar dala $150,000 daga 'yan siyasa.
"Hudu Yunusa Ari kuma an dakatar da shi ne bayan ya ayyana sakamakon zaɓen gwamna ba tare da izini ba, yayin da Farfesa Uzochukwu ya yi sakaci wajen gudanar da zaɓe, har ya ƙi sake shirya zaɓen cike gibi.

Kara karanta wannan

"Me suke shiryawa?": Ziyarar da Atiku Abubakar ya kai wa Sanata Binani ta bar baya da ƙura

Bamidele ya ƙara da cewa bisa tanadin sashe na 157(1) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999, shugaban ƙasa na da ikon tsige kwamishinoni bayan samun goyon bayan kaso biyu bisa uku na Majalisar Dattawa.

Bayan sauraron wannan jawabi ne, Majalisar dattawan ta amince da tsige kwamishinonin daga muƙamansu.

An yi musayar yawu a Majalisar dattawa

A wani rahoton, kun ji cewa an yi musayar yawu a Majalisar dattawa bayan karanta wasiƙar sauya sheƙar Sanata Ned Nwoko daga PDP zuwa APC.

Sanata Barau Jibrin da Bamidele sun yi wa Sanata Abba Moro rubdugun martani da ya yi ikirarin PDP na zaune lafiya, babu rabuwar kai a cikinta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262