Yadda Tawagar Ofishin Ribadu Suka Ceto Mata, Miji da Jaririyarsu da Aka Sace
- Jami’an tsaro na ONSA sun ceto ma’aurata da jaririyarsu mai watanni shida da ’yan bindiga suka sace a Kaduna
- An sace iyalan ne a ranar 6 ga Oktoba, 2026, lokacin da ’yan bindiga suka kutsa cikin gidajensu da misalin ƙarfe 11:30 na dare
- Bayan kuɓutar da su, an garzaya da ma’auratan da jaririyarsu zuwa cibiyar kula da lafiyar jami’an tsaro domin yi musu magani
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Rahotanni sun tabbatar da cewa an kubutar da wani mutum da matarsa tare da jaririyarsu mai watanni a duniya daga hannun yan bindiga.
Jami’an tawagar musamman ta Ofishin Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro (ONSA) ne sun ceto ma’aurata da jaririyarsu da aka sace a Kaduna.

Source: Facebook
An ceto iyalan ne a ranar Alhamis, bayan wasu ’yan bindiga sun sace su a Alrahus Estate, Millennium City, da ke ƙaramar hukumar Chikun ta jihar Kaduna, cewar TVC News.
Lamarin ya tayar da kura a Najeriya
Sace wadandan mutane biyu da jaririyarsu ya bar baya da kura inda mutane da dama ke kiran gwamnatin tarayya da ta kawo karshen lamarin.
Hakan ya biyo bayan sanya jihar Kaduna da aka sace iyalan a matsayin wacce Bola Tinubu zai kaddamar da kamfen dinsa na zaben 2027.
Mutane sun yi ta maganganu bayan sace iyalan da cewa kawai damuwar shugabanni siyasa ce ba wai kare rayukan al'umma ba.
Kulawar da ake ba ma'auratan bayan sace su
Majiyoyi masu sahihanci sun tabbatar da faruwar lamarin, inda suka bayyana cewa ana ba ma’auratan da jaririyarsu kulawar likitoci a wata cibiyar lafiya ta jami’an tsaro bayan kuɓutar da su
An sace iyalan ne a ranar 6 ga Oktoba, 2026, lokacin da wasu ’yan bindiga suka farmaki unguwar da misalin ƙarfe 11:30 na dare
Sace iyalan ya haifar da fargaba a tsakanin mazauna yankin, inda suka yi kira ga hukumomin tsaro da al’umma da su gaggauta shiga tsakani domin tabbatar da kuɓutar da su
Kuɓutar da iyalan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ƙara nuna damuwa kan satar mutane da ayyukan ’yan bindiga a jihar Kaduna, inda mazauna yankin ke kira ga jami’an tsaro da su ƙara ƙaimi wajen kare rayuka da dukiyoyi
Sace Zakka da matarsa: Atiku ya yi magana
Mun ba ku labarin cewa wani mutumi da aka yi garkuwa da shi a Kaduna, Ahmed Abubakar Zakka, na neman ɗauki bayan 'yan bindiga sun sace shi tare da matarsa da jaririyarsu suna neman Naira miliyan 300.
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar da ɗan majalisar tarayya Bello El-Rufai sun nuna damuwarsu tare da buƙatar jami'an tsaro da su gaggauta ceto su.
Bidiyon da yake yaɗuwa a kafafen sada zumunta ya nuna ɗan bindigar yana ƙoƙarin harbin Zakka a kai yayin da matarsa ke kuka tana neman ɗauki daga al'ummar Najeriya.
Asali: Legit.ng

