An Yi Hasashen Ranar da za a Yi Tashin Duniya a 2026 da Muke Ciki

An Yi Hasashen Ranar da za a Yi Tashin Duniya a 2026 da Muke Ciki

  • Wani bincike ya yi hasashen cewa yawan al’ummar duniya zai kusan kai matakin da ba shi da iyaka a ranar 13 ga Nuwamba, 2026
  • Masu binciken sun yi gargadin cewa ba yunwa ba ce za ta kashe mutane, sai dai yawan jama’a zai yi yawa har su fara rasa sararin rayuwa
  • Sai dai hasashen bai cika tafiya yadda aka tsara ba, domin yawan haihuwa a duniya ya ragu sosai tun daga shekarar 1960

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Wani binciken masana kimiyya da aka wallafa a mujallar Science a shekarar 1960 ya yi hasashen cewa duniya za ta fuskanci wani yanayi mai kama da ƙarshen zamani a ranar 13 ga Nuwamba, 2026.

Binciken ya yi hasashen cewa yawan bil’adama zai kusan kai matakin da ba zai yiwu a ƙididdige shi ba, lamarin da zai iya jefa duniya cikin matsanancin cunkoso.

Kasashen duniya
Taswirar duniya dauke da sunayen kasashe. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Hasashen ƙarshen duniya a 2026

Rahoton the Conversation ya nuna cewa wani farfesa ɗan ƙasar Austria da Amurka,Heinz von Foerster tare da ɗalibansa biyu, Patricia M. Mora da Lawrence W. Amiot, ne suka gudanar da binciken.

Sun bayyana cewa mutane sun bambanta da sauran halittu saboda iya sadarwa, haɗin kai da samar da hanyoyin magance matsaloli.

A cewarsu, waɗannan ƙwarewa na iya sa yawan al’umma ya ƙaru fiye da yadda ake tsammani, har ma ya wuce tsarin ƙaruwa na yau da kullum.

Masu binciken sun yi amfani da bayanan ƙididdigar yawan al’ummar duniya guda 24 da suka shafi tsawon shekaru 2,000 domin nuna yadda yawan mutane ke ƙaruwa a tarihi.

Bisa lissafinsu, idan aka ci gaba da samun irin wannan ƙaruwa, yawan mutane zai kusan kai matakin da ba shi da iyaka a shekarar 2026.

An ce mutane za su mutu

Masu binciken sun yi amfani da wata magana mai ban mamaki wajen bayyana hasashensu, inda suka ce jikokin jikokinmu ba za su mutu saboda yunwa ba, amma za a matse su har su mutu.

Sun yi nuni da cewa ƙaruwar jama’a za ta iya haifar da matsalar ƙarancin sararin zama da albarkatun da ake buƙata domin rayuwa.

Sai dai sun kuma bayyana cewa haɗin kai da sadarwa da suka taimaka wa bil’adama wajen samun ci gaba za su iya zama hanyar kauce wa wannan barazana.

A cewarsu, ya kamata duniya ta yi aiki tare wajen rage yawan haihuwa da kusan rabin abin da ake samu, maimakon ƙoƙarin rage tsawon rayuwar mutane.

Heinz von Foerster
Wanda ya yi hasashen tashin duniya, Heinz von Foerster. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Hasashen ya samu karɓuwa a duniya

Bayan wallafa binciken, ya jawo hankalin kafafen yaɗa labarai da masana kimiyya. Mujallar Time da jaridar The New York Times sun wallafa rahotanni kan hasashen.

Wasu mutane sun ɗauki binciken a matsayin barkwanci kan fargabar ƙaruwar yawan jama’a, amma wasu masana sun yi nazari mai zurfi kan lissafin da aka yi amfani da shi.

An samu wasiƙu daga masana lissafi da ƙididdigar al’umma da suka soki binciken, inda suka bayyana wasu daga cikin ƙudurorinsa a matsayin marasa ma’ana.

Daga shekarun 1960 zuwa 1980, ana ci gaba da ambaton wannan hasashe a littattafan kimiyya da suka shafi halittu, muhalli da ƙididdigar yawan al’umma.

Me ya sa hasashen bai cika ba?

Duk da cewa hasashen ya yi daidai da ƙididdigar yawan al’umma na wasu shekaru, lamarin ya fara sauyawa kusan shekarar 1993, lokacin da ƙaruwa a yawan al’ummar duniya ta fara yin ƙasa da abin da masu binciken suka yi hasashe.

A yau, yawan haihuwa a duniya ya ragu zuwa ƙasa da rabin matakin da aka samu a shekarar 1960.

Wannan na nuna cewa mutane sun fara samun sauyin da masu binciken suka ba da shawarar a yi domin rage haɗarin da suke hasashe.

Saboda haka, duk da kusancin ranar 13 ga Nuwamba, 2026, babu wani tabbaci na kimiyya da ke nuna cewa ƙarshen duniya zai zo a wannan rana.

Agogon tashin duniya ya motsa

A wani labarin, mun ruwaito cewa masana kimiyya sun yi gargadin cewa duniya na ƙara fuskantar barazana, bayan da agogon ƙarshen duniya ya ƙara matsowa da daƙiƙa 85.

An danganta wannan gargadi da ƙaruwa a barazanar amfani da makaman nukiliya, sauyin yanayi da kuma ci gaban fasahohin zamani kamar basirar AI.

Masana sun kuma bayyana cewa rashin haɗin kai tsakanin ƙasashe da yaɗuwar bayanan ƙarya na ƙara tsananta haɗarin da mutane ke fuskanta a duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng