'Sai Masu Biyayya': An Ware Ƴan APC da Za a ba Motoci a Kamfen Tinubu
- Jam’iyyar APC a jihar Abia ta sanya ranar 16 ga Nuwamba, 2026, domin ƙaddamar da gangamin neman sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu a 2027
- Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Benjamin Kalu, ya sanar da shirin rabon motoci sama da 100 ga mambobin APC masu biyayya ga jam’iyyar
- Shugabannin APC sun kafa kwamitoci daban-daban domin kula da harkokin tsaro, sufuri, yaɗa labarai da tattara magoya baya a faɗin jihar Abia
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Umuahia, Abia - Jam'iyyar APC a jihar Abia ta shirya gudanar da babban gangamin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin sake zaɓensa a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Jam’iyyar ta sanya ranar 16 ga Nuwamba, 2026, domin gudanar da taron wanda za a yi a filin wasa na Umuahia.

Kara karanta wannan
Shugaban INEC ba ya son a fitar da takardun Tinubu, ya shigar da bukata gaban kotu

Source: Twitter
Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Benjamin Okezie Kalu, ne ya bayyana hakan yayin wani muhimmin taron shugabannin jam’iyyar da aka gudanar a ranar Talata, 10 ga Nuwamba, a gidansa da ke ƙaramar hukumar Bende, cewar Tribune.
Kalu, wanda kuma shi ne mataimakin daraktan yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC a yankin Kudu, ya buƙaci shugabannin jam’iyyar da su fara tattara magoya baya tun da wuri domin tabbatar da samun jama’a da dama a wajen gangamin.
APC za ta raba motoci sama da 100
Ɗaya daga cikin muhimman bayanan da Kalu ya bayyana a taron shi ne shirin raba motoci sama da 100 ga wasu mambobin jam'iyyar APC da suka nuna jajircewa da biyayya ga jam’iyyar.
Ya ce za a gudanar da rabon motocin ne a yayin gangamin, domin nuna godiya ga mutanen da suka bayar da gudunmawa wajen bunƙasa jam’iyyar.
Mataimakin Kakakin Majalisar ya kuma yi kira ga sauran mambobi da su ci gaba da kasancewa masu biyayya da kuma ba da gudunmawa wajen cimma manufofin APC.
A cewarsa, jam’iyyar na buƙatar haɗin kai da kyakkyawan tsari a dukkan matakan shugabancinta domin samun gagarumar nasara a zaɓen 2027.

Source: Facebook
APC ta kafa kwamitoci domin shirya gangamin
Domin tabbatar da nasarar taron, shugabannin APC sun kafa kwamitoci daban-daban da za su kula da muhimman ayyukan da suka haɗa da tattara magoya baya, sufuri, tsaro, yaɗa labarai da harkokin gudanarwa.
Shugaban APC na jihar Abia, Chijioke Chukwu, wanda kuma shi ne kodinetan yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa a jihar, ya yi kira ga mambobin jam’iyyar da ke ƙananan hukumomi 17 da su halarci gangamin.
Ya bayyana cewa taron zai kasance wata dama ta nuna ƙarfin jam’iyyar da kuma irin shirin da take yi domin zaɓen 2027, cewar Punch.
Gangamin na ranar 16 ga Nuwamba na zuwa ne a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin APC na ƙarfafa goyon bayan da take samu a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya, musamman wajen neman sake zaɓen Tinubu.
Tinubu ya sake daukar alkawari
An ji cewa Bola Tinubu ya yi alƙawarin samar da wutar lantarki mai ɗorewa da rage tsadar rayuwa idan ya sake samun nasara a zaɓen 2027.
Ya ce gwamnatinsa za ta tallafa wa ƙananan masana’antu da sana’o’i domin bunƙasa tattalin arziki da samar da ayyukan yi.
Shugaban ƙasar ya yi wannan alƙawarin ne yayin gangamin APC a Dutse, inda ya sake tuna wa ’yan Najeriya alkawarin inganta wutar lantarki na 2023.
Asali: Legit.ng

