"Atiku Shi Kadai Ya Aikata Abinda Kowa Ya Kasa Yi Tun 1999": Fani-Kayode Ya Yi Zolayi Tsohon 'VP'

"Atiku Shi Kadai Ya Aikata Abinda Kowa Ya Kasa Yi Tun 1999": Fani-Kayode Ya Yi Zolayi Tsohon 'VP'

  • Tsohon minista kuma jigo a jam’iyyar APC, Femi Fani-Kayode ya yi shagube ga Atiku kan yadda ya taimaki APC
  • Fani-Kayode ya yi shaguben ne ga Atiku Abubakar a shafinsa na Twitter a ranar Juma'a 12 ga watan Mayu
  • Fani-Kayode ya ce Atiku na bin ‘yan Najeriya bashin godiya tun da ya nakasa musu jam’iyyar PDP

FCT, Abuja - Jigo a jam’iyya mai mulki ta APC, Femi Fani-Kayode ya yi ba’a ga tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa a zaben da ya wuce, Atiku Abubakar.

Fani-Kayode wanda tsohon minista ne a Najeriya ya ce Atiku na bin ‘yan Najeriya bashin godiya saboda yadda ya nakasa musu jam’iyyar PDP har kwano.

fani-kayode
Femi Fani-Kayode, Hoto: Facebook
Asali: Facebook

Tsohon ministan ya yi wannan shaguben ne a shafinsa na Twitter a ranar Juma’a 12 ga watan Mayu, kamar yadda Legit.ng Hausa ta gano.

Kara karanta wannan

Daf da Zai Bar Mulkin Najeriya, Buhari Ya Amince a Kafa Sabuwar Jami'ar Tarayya

Ya kara da cewa Atiku ya yi bajintar da ‘yan Najeriya ya kamata su biya shi musamman lokacin zaben shugaban kasa da ya gabata ganin yadda ya kashe PDP yana kokarin saka ta a rami’

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fani-Kayode ya rubuta a shafinsa kamar haka:

A cewar Kayode:

“Abu daya da ba zamu iya dauka a wurin Atiku ba, Wazirin Adamawa shine, shi kadai ya yi abinda babu mai iyawa tun 1999: saboda ya nakasa mana PDP kuma ya binne ta, yadda ba za ta tashi ba. Wannan kadai ya kamata ‘yan Nigeria su gode masa.”

Tsohon ministan ya kasance jigo a jam’iyyar APC musamman a kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa da aka yi, inda Bola Tinubu ya ci zaben.

Tun bayan sanar da sunan Bola Tinubu a matsayin zababben shugaban kasa, Atiku Abubakar bai yarda da ya fadi ba, har yanzu yana kan bakansa kuma ya ce akwai haske a kotun zabe.

Kara karanta wannan

Barazanar Sanatocin Jihohin Arewa Ya Jawo APC Ta Ji Uwar Bari a Kan Takarar Majalisa

Tuni har an fara sauraran korafe-korafen zaben shugaban kasa a ranar Litinin 8 ga watan Mayu.

Atiku Ya Ce Har Yanzu Bai Yadda Ya Fadi Ba

A wani labarin, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubkar ya ce har yanzu bai yarda da ya fadi zaben da aka gudanar ba, domin murdiya aka tafka.

Atiku ya bayyana haka ne a taron liyafar da kungiyar gwamnonin jam'iyyar PDP suka shirya don taya zababbun 'yan takarar jam'iyyar murnar lashe zabe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel