Masussuka: Izala ta yi barazanar kai Sheikh Dangugu kotu idan bai janye maganarsa ba

Masussuka: Izala ta yi barazanar kai Sheikh Dangugu kotu idan bai janye maganarsa ba

Kaduna - Maganganun da Sheikh Usman Dangungu ya yi dangane da kisan Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka sun jefa shi a matsala.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’iqamatis Sunnah (JIBWIS) ta sanar da cewa ta buƙaci malamin ya janye kalaman da ya yi.

A shafinta na Facebook, ƙungiyar Izala ta bayyana cewa ta aika wa Usman Dangugu takardar kashedi domin ya lashe aman shi.

Ana zargin malamin da zargin Izala da hannu wajen mutuwar Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka, wanda ‘yan ta’adda suka bindige shi.

Izala ta kuma nemi malamin addinin ya nemi afuwarta a gaban duniya tare da shan alwashin ba zai sake jifar ta da irin wannan zargi ba.

An fito da takardar ne a ranar Litinin 9 ga watan Nuwamba 2026 kuma ana neman Usman Dangugu ya nemi afuwa nan da mako guda.

Idan tsawon wa’adin ya wuce ba tare da Sheikh Dangugu ya yi abin da aka buƙata ba, lauyoyin Izala za su gurfanar da shi a gaban alƙali.

Kara karanta wannan

Matsaloli 10 da Sheikh Isa Pantami ya tsallake wajen zama ‘dan takarar gwamna a Gombe

Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’iqamatis Sunnah ta ja hankalin jama’a cewa zargin da aka yi ya girmama kuma ya kai matakin shari’a.

Ibrahim Umar Abere ya sa hannu a takardar a madadin kamfanin lauyoyin Umar Attorneys da yake kan titin jami’ar Bayero a garin Kano.

Kamar yadda Ibrahim Umar Abere ya bayyana, ana sa rai malamin ba zai dauki takardar da wasa ba.

Lauyoyin ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’iqamatis Sunnah (JIBWIS) sun aika wa Sheikh Usman Dangungu takardar gargadi ta shari'a mai taken Letter of Demand to Withdraw Defamatory Statement. A cikin takardar, lauyoyin ƙungiyar sun buƙaci Sheikh Usman Dangungu ya janye kalaman da ake zargin ya yi na danganta ƙungiyar IZALA da kisan Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka, tare da neman gafara a bainar jama'a da kuma ɗaukar alƙawarin cewa ba zai sake maimaita irin waɗannan zarge-zarge ba tare da sahihiyar hujja ba. Takardar ta ba shi wa'adin kwanaki bakwai (7), daga ranar da ya karɓe ta, domin ya cika waɗannan buƙatu. Idan har wa'adin ya cika ba tare da bin umarnin ba, ƙungiyar ta bayyana aniyarta ta ɗaukar matakin shari'a domin kare mutuncinta da martabarta. LURA: Wannan batu ya wuce muhawarar kafafen sada zumunta. Yanzu ya shiga matakin shari'a, inda doka za ta taka rawar gani wajen warware takaddamar.

Kara karanta wannan

Gwamna ya yi magana mai zafi kan harin da aka kai wa ayarin Peter Obi da Kwankwaso

Jibwis Nigeria

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng