Atiku Ya Ce Ya Gano Tarkon da Tinubu Ya Kafa Masa kan Bashin da zai Ciwo
- Tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya yi watsi da shirin gwamnatin tarayya na karɓar bashin $500m daga Bankin Duniya.
- Atiku ya bayyana cewa gwamnatin Bola Tinubu ba ta da 'yancin kulla sabon alƙawarin bashi dab da zaɓen shugaban ƙasa da kuma mika mulki na shekarar 2027.
- Sanarwar ta fito ne ta hannun Phrank Shaibu, Daraktan Sadarwa na Yaƙin Neman Zaɓen Atiku, wanda ya bayyana cewa daukar bashin zai jefa ƙasar cikin bautar tattalin arziƙi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya jaddada rashin amincewarsa da shirin gwamnatin tarayya na neman sabon bashi na dalar Amurka miliyan 500 daga Bankin Duniya.

Kara karanta wannan
"Ko a jiki na," Atiku ya maida martani bayan kotu ta rushe takararsa a zaben 2027
Atiku ya bayyana cewa bai kamata shugaba Bola Tinubu ya kulla alƙawarin sabon bashi ba a daidai lokacin da yake shirin mika mulki a shekarar 2027.

Source: Facebook
Vanguard ta rahoto cewa matsayin Atiku ya biyo bayan rahotannin da ke cewa gwamnatin tarayya na neman tallafin Bankin Duniya don kafa tsarin INFRAGROW.
Matakin da Atiku zai dauka
A cikin wata sanarwa da Darakta Janar na Sadarwa na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Atiku, Phrank Shaibu ya fitar, Atiku ya gargadi gwamnatin tarayya game da matakin.
Ya rubuta cewa:
“Wani shugaban ƙasa da ke shirin barin gado ba shi da hakkin ɗaura wa sabon shugaban kasa sabon bashi kwanaki kaɗan kafin mika mulki.
"Idan har wannan gwamnatin ta tsara yi wa makomar Najeriya mummunan rauni, mu ba za mu amince da hakan ba.”
Batun kafa gwamnati a 2027
Atiku ya ƙara da cewa a ranar 16 ga Janairu, 'yan Najeriya za su zaɓi sabuwar hanyar gudanar da mulki wadda za ta ba da damar sauƙaƙa rayuwa ba wai wadda za ta riƙa bin bashin da ba a yi wa al'umma bayanin sharudansa a sarari ba.

Kara karanta wannan
Nafiu Bala ya fito yana murna da rusa takarar Atiku da dukkan 'yan ADC a Najeriya
A cewar rahoton, an tsara yin la'akari da shirin bashin dala miliyan 500 a ranar 25 ga Mayu, 2027, wato kwana huɗu kacal kafin rantsar da sabon shugaban ƙasa.
Daily Trust ta rahoto Atiku ya ce:
“Kamar yadda kararin maganar Swahili ke gargadi, 'Idan ka ba da aron kafafun ka ga wani, zaka je inda ya jagorance ka ne.'
"Shugaban da ya karɓi bashi yana daf da sauka ya bar wanda zai gaje shi ne a kan kafafun mai kudin da aka karbo bashin. Ina kira ga Bankin Duniya da kada ya amince da wannan bashi da ake shirin amincewa da shi.”

Source: Facebook
Za a shiga jihohi tallata Tinubu
A wani labarin, kun ji cewa ƙungiyar tallata Tinubu karkashin jagorancin Tompolo ta sanar da faɗaɗa yakin neman zaɓen shugaba Tinubu zuwa jihohi takwas tsakanin 9 zuwa 14 ga Nuwamba.
Wannan yaƙin neman zaɓe ya haɗa da jihohin Enugu, Cross River, Bayelsa, Zamfara, Jigawa, Anambra, Kebbi da kuma Abia a sassan Kudu maso Gabas, Kudu maso Kudu da kuma Arewa maso Yamma.
A cewar jadawalin da ƙungiyar ta fitar, shirin ya fara ne a ranar Litinin tare da gudanar da taro a jihohin Enugu da Cross River domin fadada yakin neman zaben.
Wanda ya tantance Ibrahim Yusuf, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng