Hatsabibin Ɗan Bindiga da Ya Addabi Jama'a Ya Sheƙa Barzahu a Katsina
- Rahotanni sun bayyana cewa an kashe fitaccen shugaban ’yan bindiga yayin musayar wuta tsakanin ƙungiyoyin ’yan bindiga a jihar Katsina
- An ce lamarin ya faru ne a wani daji da ke ƙaramar hukumar Faskari a yammacin ranar Litinin 9 ga watan Nuwambar 2026
- Wani manazarci kan harkokin tsaro ya bayyana cewa marigayin ya shahara wajen satar manoma tare da tilasta musu yin aiki a gonakinsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Katsina – Rahotanni sun nuna cewa an kashe wani fitaccen shugaban ’yan bindiga, Kachalla Bello, a wani artabu da ya barke.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa an samu matsala tsakanin wasu ƙungiyoyin ’yan bindiga masu hamayya da juna a jihar Katsina.

Source: Original
Wakilin Legit Hausa ya samu wannan rahoto ne daga shafin X na Bakatsine da ke sharhi kan lamuran tsaro a Arewacin Najeriya.
Lamarin ya faru ne a wani daji da ke ƙaramar hukumar Faskari a yammacin ranar Litinin, 9 ga watan Nuwamba, 2026.
Abin da aka sani game da Kachalla Bello
A cewar rahotanni, Kachalla Bello ya kasance cikin ’yan bindigar da suka addabi al'ummomin karkara ta hanyar kai hare-hare da satar mutane.
An bayyana cewa ɗan bindigar ya shahara wajen sace mutane daga gonakinsu, inda yake tilasta musu yin aikin gona a gonakinsa kafin daga bisani ya sake su.
Masanin ya ce irin wannan hali da ayyukan shugaban ’yan bindigar sun jefa mazauna yankunan da abin ya shafa cikin matsanancin wahala da fargaba.
Sai dai har zuwa lokacin da aka wallafa wannan rahoto, babu cikakken bayani daga hukumomin tsaro da ya tabbatar da mutuwar Kachalla Bello.
Yadda dan ta'adda ya mutu
Rahoton ya nuna cewa mutuwar Kachalla Bello ta biyo bayan wani mummunan artabu da ya haɗa ƙungiyoyin ’yan bindiga biyu masu gaba da juna a cikin daji.
Lamarin ya sake jawo hankali kan rikicin da ke faruwa tsakanin ƙungiyoyin ’yan bindiga a wasu sassan jihar Katsina, musamman yadda ayyukansu ke ci gaba da shafar rayuwar al'ummomin karkara.
Karin bayani na tafe.....
Asali: Legit.ng

