Bayan Kwace Ikon Majalisa, an Fara Shirin Tsige Jami'in Trump kan Yakin Iran

Bayan Kwace Ikon Majalisa, an Fara Shirin Tsige Jami'in Trump kan Yakin Iran

  • Shugaban marasa rinjaye a Majalisar Wakilan Amurka, Hakeem Jeffries, ya bayyana goyon bayansa ga ƙudirin tsige Ministan Tsaro, Pete Hegseth, kan yaƙin Iran
  • Jeffries ya zargi Hegseth da amfani da muƙaminsa ba bisa ƙa’ida ba, raunana tsaron ƙasar da kuma jefa Amurka cikin yaƙin da ya yi tsada
  • Biyo bayan lamarin, shugaban Amurka, Donald Trump, ya kare ministan, inda ya buƙaci ’yan majalisa su goyi bayansa maimakon tsige shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Amurka – Shugaban marasa rinjaye a Majalisar Wakilan Amurka, Hakeem Jeffries, ya bayyana cewa jam’iyyar Democrat na shirin goyon bayan ƙudirin tsige Ministan Tsaro, Pete Hegseth, kan rawar da ya taka a yaƙin Iran.

Jeffries ya bayyana matsayarsa ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a shiri na musamman bayan cin zaben da jam'iyyarsa ta yi.

Kara karanta wannan

Dan takara ya ce zai kifar da Tinubu saboda dogara ga Allah a 2027

Pete Hegseth a Amurka
Ministan tsaron amurka, Pete Hegseth. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Jaridar The Independent ta rahoto cewa Jeffries ya yi wannan furuci ne bayan an tambaye shi ko jam’iyyar Democrat za ta gudanar da bincike kan ministan idan ta sake samun rinjayen kujeru a majalisun dokokin Amurka.

An goyi bayan ƙudirin tsige Hegseth

Da aka tambaye shi ko zai goyi bayan ƙudirin tsige ministan, Jeffries ya ce babu shakka yana goyon bayansa, yana mai cewa ya kamata Hegseth ya bar muƙaminsa.

Ya zargi ministan da yin amfani da ikon da aka ba shi ta hanyar da ba ta dace ba, tare da raunana tsaron ƙasar.

Jeffries ya kuma ce Hegseth ne ya jagoranci shigar Amurka cikin yaƙin Iran wanda ya bayyana a matsayin wanda aka zaɓi shiga ba tare da larura ba, kuma ya jawo wa ƙasar asarar kuɗi masu yawa.

A cewarsa, yaƙin ya ƙara tsadar rayuwa ga Amurkawa tare da rage tsaron ƙasar ba tare da wata hujja ba.

Kara karanta wannan

Wuta ko aljanna: Donald Trump ya fadi a ina zai iya kasancewa a lahira

Za a gabatar da ƙudirin tsige ministan

Wani ɗan majalisar wakilai na jam’iyyar Republican daga jihar Kentucky, Thomas Massie, ya bayyana shirin gabatar da ƙudirin tsige Hegseth tun ranar Litinin.

Masu adawa da ministan na zargin cewa ya bayar da umarnin kai hare-haren sama na Operation Epic Fury kan Iran da aka fara ranar 28 ga Fabrairu, ba tare da neman amincewar Majalisar Dokoki ba.

Sun ce hakan ya saɓa wa dokar yaki ta shekarar 1973, wadda ta tanadi rawar da Majalisa ke takawa wajen amincewa da matakan yaƙi.

Trump ya kare Hegseth

A nasa ɓangaren, shugaban Amurka, Donald Trump, ya fito ya kare Hegseth bayan Massie ya ɗauki matakin neman a tsige shi.

Shugaba Donald Trump
Shugaba kasar Amurka, Donald Trump. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Trump ya bayyana Massie a matsayin wanda ya sha kaye a siyasa, yana mai cewa yana ƙoƙarin tsige ɗaya daga cikin jami’an soji da ya kira masu farin jini da nasara a ƙasar.

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Donald Trump ya ce ya kamata a yaba wa Hegseth maimakon a tsige shi.

Kara karanta wannan

Yakin Iran: Matsala ta tunkaro gwamnatin Trump, an shirya tsige mukarrabansa

Rasha za ta sayar wa Iran makami

A wani rahoton, an bayyana cewa Rasha ta amince ta samar wa Iran da na’urorin harba makamai masu linzami guda 90 a ƙarƙashin wata yarjejeniya da ƙasashen biyu suka kulla.

Yarjejeniyar ta ƙara nuna yadda dangantakar soji tsakanin Moscow da Tehran ke ƙara ƙarfi duk da matsin lambar da ƙasashen Yamma ke yi wa Iran da Rasha.

Rahoton ya fito ne bayan wani babban jami’in tsaron Iran ya ziyarci shugaban Rasha, Vladimir Putin, domin tattauna hanyoyin faɗaɗa haɗin gwiwar tsaro tsakanin ƙasashen biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng