"Abin da Zai Sa Tinubu Ya Samu Gagarumar Nasara a Zaben Shugaban Kasa na 2027"

"Abin da Zai Sa Tinubu Ya Samu Gagarumar Nasara a Zaben Shugaban Kasa na 2027"

  • Tsohon gwamnan Abia, Orji Uzor Kalu, ya ce Shugaba Bola Tinubu zai lashe zaben shugaban kasa na 2027 da gagarumar nasara
  • Sanatan ya kare sauye-sauyen tattalin arzikin Tinubu, yana mai cewa tattalin arzikin Najeriya ya samu daidaito a matakin kasa
  • Kalu ya ce babban kalubalen gwamnati yanzu shi ne mayar da wannan daidaito zuwa ci gaban tattalin arziki da jama’a za su amfana da shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Tsohon gwamnan Jihar Abia kuma sanatan da ke wakiltar Abia ta Arewa, Orji Uzor Kalu, ya kare manufofin sauye-sauyen tattalin arzikin Shugaba Bola Tinubu.

Sanata Kalu ya kuma yi hasashen cewa mai girma Tinubu zai lashe zaben shugaban kasa na 2027 da gagarumar nasara.

Kalu.
Sanata Orji Uzor Kalu a ofishinsa da ke zauren Majalisar dattawa a Abuja Hoto: Orji Uzor Kalu
Source: Facebook

Kalu ya bayyana hakan ne ranar Litinin yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Arise PrimeTime, shahararren shirin tattaunawa kan al’amuran yau da kullum na gidan talabijin din Arise News.

Kara karanta wannan

Abokin takaran Atiku ya bayyana dalilin rabuwa da shi ya kama layin Tinubu a APC

Kalu ya kare tsare-tsaren Tinubu

Kalu, wanda a yanzu yake shugabantar kwamitin Majalisar Dattawa kan Hukumar Raya Kudu maso Gabas, ya kare gwamnatin Tinubu daga sukar da ake yi mata kan tsadar rayuwa da matsin tattalin arzikin da sauye-sauyen da take aiwatarwa suka haifar.

Ya ce Tinubu ya yi nasarar daidaita tattalin arzikin Najeriya a matakin kasa baki daya, amma har yanzu akwai sauran aiki wajen tabbatar da cewa wannan ci gaba ya kai ga gidajen jama’a da harkokin kasuwanci.

A cewarsa, babban aikin da ke gaban gwamnati yanzu shi ne mayar da daidaiton tattalin arzikin da aka samu zuwa ci gaba na zahiri, karuwar masana’antu, samar da ayyukan yi da inganta rayuwar al’umma.

“Shugaba Tinubu ya yi nasarar daidaita tattalin arzikin nan a matakin kasa. Abin da muke kokarin shawo kansa yanzu, shi ne matsalolin da ke matakin kasa da kasa da kuma rayuwar jama’a,” in ji shi.

Ya kuma yabawa Tinubu kan inganta alakar tattalin arzikin Najeriya da sauran kasashe, yana mai cewa kasar na kara jan hankalin masu zuba jari na kasashen waje.

Kara karanta wannan

"Makomar matasan Najeriya ta dogara da wanda za su zaɓa a babban zaben 2027"

Kalu ya hango nasarar Tinubu

Sanatan ya nuna kwarin gwiwar cewa Tinubu zai samu wa’adi na biyu, inda ya bayyana jam’iyyun adawa a matsayin wadanda ba su da cikakken tsari a siyasance.

Ya kuma tabbatar da cewa hasashensa ba zai gaza ba, yana mai cewa karfin APC a zabe bai tsaya kan farin jinin shugaban kasa kadai ba.

“Shugaba Tinubu zai yi nasara. Shugaba Tinubu ba shi da abokin hamayya. Karfin APC a zabe ya wuce mutum ko halin shugaban kasa. Jam’iyya mai mulki tana da babban tsarin siyasa da kuma dimbin magoya baya a matakin kasa.
“Abin da muke gani a kafafen sada zumunta ba shi ne ainihin abin da ke faruwa a kasa ba. Jam’iyyarmu babba ce matuka, kuma tana da dimbin magoya baya. Muna da mutane da yawa da ke goyon bayan jam’iyyar,” in ji shi.
Bola Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a wurin taro a Abuja Hoto: @OffialABAT
Source: Twitter

Ya kara da cewa ’yan majalisar APC da sauran masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa sun fara kokarin karfafa tasirin jam’iyyar a mazabunsu domin tabbatar da sake zaben Tinubu.

Kara karanta wannan

“Ko zai shafi Tinubu a 2027?” Yadda al’ummar Legas suka tarbi Kwankwaso ya ja hankali

Kalu ya kafa sharadin barin APC

Kun ji cewa sanatan da ke wakiltar Abia ta Arewa a Majalisar dattawa, Orji Kalu, ya vayyana cewa zai iya yin murabus daga jam’iyyar APC.

Sanata Kalu ya ce a shirye yake ya bar APC matukar aka kawo masa inda Shugaba Tinubu ya taba nuna rashin girmamawa ga cocin Katolika.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262