Majalisar Dattawa: Jam’iyyar APC Ta Fadi Makomar Akpabio bayan Cikar Wa'adinsa
- Nentawe Yilwatda ya ce sanatocin da za su ci zaɓen 2027 ne za su yanke shawarar wanda zai zama shugaban Majalisar Dattawa
- Wannan na nufin Godswill Akpabio ba shi da tabbacin ci gaba da riƙe muƙamin, duk da goyon bayan da wasu sanatoci suka nuna masa
- Shugaban APC na ƙasa ya bayyana cewa kujerar da ke gaban jam’iyyarsu a shekara mai zuwa ita ce ta shugaban marasa rinjaye kawai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda ya yi magana game da shugabancin majalisa ta 11 da za a kafa a Yunin 2027.
Farfesa Nentawe Yilwatda ya ce sanatoci ne za su yanke shawarar ko Godswill Akpabio zai ci gaba da zama shugaban majalisar dattawa lokacin.

Source: Twitter
Matsayin shugabannin APC a zaben Majalisar tarayya
Nentawe Yilwatda ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels TV ranar Litinin.
Ya ce shugabancin APC ba shi da wani ɗan takara da yake goyon baya a yanzu, domin sanatocin da za su ci zaɓe ne za su zaɓi wanda suke so.
Farfesa Yilwatda ya ce:
"Sanatoci ne za su yanke wannan hukunci. Mu jira a fara gudanar da zaɓe.
A gaskiya, ba ni da wani mutum da nake so a yanzu. Sanatoci ne za su zaɓi wanda suke so ya zama shugaban majalisar dattawa.
"Abin da jam’iyya za ta yi kawai shi ne zaɓen shugaban masu rinjaye."
Shugaban APC ya ƙara da cewa majalisa ta 11 za ta fara aiki ne a watan Yunin 2027, bayan kammala babban zaɓen ƙasar a farkon shekara.
Gasar neman shugabancin Majalisar dattawa
Akpabio, wanda ya zama shugaban majalisar dattawa a watan Yunin 2023, yana neman ci gaba da riƙe wannan muƙami bayan zaɓe mai zuwa.
A watan Oktoban da ya gabata, wasu sanatoci sun bayyana goyon bayansu ga sake zaɓen Akpabio, inda suka nuna cewa babu gurbi a majalisar.
Sai dai ana ganin akwai yiwuwar fuskantar hamayya daga wasu manyan 'yan siyasa musamman idan Hope Uzodinma ya samu yadda yake so.
Daily Trust ta ce ana raɗe-raɗin cewa yana da sha'awar zama shugaban Majalisar Dattawa duk da bai kammala wa'adinsa na gwamna a Imo ba.
Haka kuma, ana danganta Sanata Adams Oshiomhole, mai wakiltar Edo ta Arewa, da sha'awar neman wannan kujera da Akpabio yake kai.
A halin yanzu, APC ce ke da rinjayen kujeru a Majalisar dattawar dattawa mai sanataoci 109 kuma za ta so a cigaba da tafiya a hakan bayan zaɓe.

Source: Twitter
Muktar Betara ya kashe wa 'yan majalisa N1bn
An ji yadda Hon. Muktar Betara ya jawo alamar tambaya da ya raba wa ‘yan majalisan APC fiye da N1bn da sunan kamfen 2027 a jihar Borno.
'Dan siyasar ya ware Naira miliyan 50 ga kowane ɗan takarar majalisar tarayya, da miliyan 20 ga masu harin zuwa Majalisar dokoki ta jiha.
Masu sharhi sun nemi a binciki tushen kuɗin ganin an san yana harin zama shugaban majalisa tun ba yau ba.
Asali: Legit.ng