Jami'an Tsaro Sun Dakile Yunkurin Kone Ofishin 'Yan Sanda, Sun Kame 'Yan Ta'adda 12

Jami'an Tsaro Sun Dakile Yunkurin Kone Ofishin 'Yan Sanda, Sun Kame 'Yan Ta'adda 12

- Rundunar 'yan sanda ta dakile yunkurin kona ofishin 'yan sanda a wani yankin jihar Legas

- Rahoto ya bayyana cewa, rikici ne ya barke tsakanin wasu mutane, lamarin da ya jawo rasa rai

- Sai dai, rundunar ta yi aiki tukuru wajen tabbatar da an kwantar da tarzomar tare da kame wasu

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Legas ta ce an yi kokarin lalata ofisoshinta biyu a cikin jihar, TheCable ta ruwaito.

Rikici ya barke a yankin Ile-Epo na Legas ranar Litinin, yayin da masu zanga-zanga suka yi tattaki zuwa ofishin ‘yan sanda da ke yankin kan zargin kisan wani mutum da aka ce shi dan acaba ne, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Wani mazaunin garin, wanda ya zanta da NAN, ya yi zargin cewa babbar mota ce ta kashe mai babur din.

KU KARANTA: Mutum Biyu Sun Mutu, 11 Sun Jikkata Sakamakon Fashewar Gas a Bauchi

'Yan Sanda Sun Dakile Yunkurin Kone Ofishinsu, Sun Kame 'Yan Ta'adda 12
'Yan Sanda Sun Dakile Yunkurin Kone Ofishinsu, Sun Kame 'Yan Ta'adda 12 Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Da yake magana a kan lamarin, Olumuyiwa Adejobi, mai magana da yawun ‘yan sanda na Legas, a cikin wata sanarwa a ranar Litinin, ya ce an yi yunkurin kona ofishin amma 'yan sanda sun dakile harin kuma sun kame mutane 12.

Adejobi ya kara da cewa ‘yan sanda sun kuma dakile sake kai hari a wani ofishi a yankin Elemoro.

“Rundunar‘ yan sanda reshen jihar Legas ta yi dabara ta fatattaki wasu ‘yan daba wadanda suka yi yunkurin banka wa sashen Oke Odo na rundunar wuta a yau 24 ga watan Mayu, 2021 kuma an kame 12 daga cikinsu.

"Rundunar tana son bayyanawa a sarari cewa ba a rasa rai ba kuma ofishin ‘yan sanda bai kone ba,” in ji sanarwar.

Hakazalika ya bayyana cewa, an shawo kan lamarin, kuma tuni mutane kowa ya koma harkokinsa.

KU KARANTA: Badakala: Majalisa Na Neman Akanta-Janar, Da Sauransu Kan Gibi a Kudaden da Aka Kwato

A wani labarin, An kama wasu mutane hudu da ake zargi ‘yan fashi da makami ne da suka yi awon gaba da wata tirela mai dauke da fulawar Golden Penny kan babban titin Shagamu-Ijebu Ode na jihar Ogun.

Wadanda ake zargi da satar kayayyakin a ranar 16 ga Afrilu sun shiga hannun rundunar ‘yan sanda ta Jihar Ogun a ranar 5 ga Mayu, kamar yadda hukumomin 'yan sanda suka tabbatar wa gidan Talabijin na Channels a ranar Litinin.

A cewar wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Abimbola Oyeyemi ya fitar, an ce wadanda ake zargin sun hada da Eze Anthony Sopruchuckwu, Eze Chijoke Edeh, Olalekan Ayodele Muritala da Samuel Johnson.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.