Gwamna Ya Tara Damin Miliyoyin Naira, Ya Raba wa 'Yan Kasuwa
- Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya raba tallafin Naira miliyan 143 ga ’yan kasuwa 76 da gobara ta shafa a tsohuwar kasuwar Sokoto da tashar mota
- Shugaban kwamitin tantance waɗanda gobarar ta shafa ya ce tallafin ba diyya ba ne, illa taimako ne domin bai wa ’yan kasuwar damar farfaɗo da harkokinsu
- Gwamnatin Sokoto ta ce an tantance masu neman tallafin 94, amma mutum 76 ne aka tabbatar sun kasance waɗanda gobarar ta shafa da gaske
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma ƙwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Sokoto – Gwamnatin jihar Sokoto ta raba tallafin Naira miliyan 143 ga ’yan kasuwa 76 da gobara ta shafa a tsohuwar kasuwar Sokoto da tashar mota domin taimaka masu su farfaɗo da harkokinsu.
Gwamna Ahmed Aliyu ya cika alƙawarin da ya ɗauka na tallafa wa waɗanda lamarin ya shafa, wanda ya yi a ranar Juma'a, 9 ga Oktoba, bayan karɓar rahoton kwamitin da ya kafa domin binciken gobarar.

Kara karanta wannan
Minista ya ɓallo ruwa a gaban ƙasashen duniya, ya yi maganar da ka iya juyo wa kan Tinubu

Source: Facebook
Gwamnatin jihar ta wallafa a Facebook cewa an bai wa waɗanda aka tantance a matsayin waɗanda gobarar ta shafa da gaske kuɗin tallafin domin su sake buɗe kasuwancinsu.
Adadin kuɗin da aka raba
Shugaban kwamitin da aka kafa domin binciken gobarar, Barista Gandi Umar Muhammad, ya bayyana jin daɗinsa kan yadda aka gudanar da rabon tallafin.
Ya kuma yaba wa ’yan kasuwar da abin ya shafa saboda haɗin kai da suka bayar yayin gudanar da aikin tantancewa da rabon kuɗin.
A cewarsa, mafi yawan kuɗin da aka bai wa mutum guda sun kai Naira miliyan 25, yayin da aka ƙayyade na sauran waɗanda suka amfana bisa girman asarar da kowannensu ya yi.
Gandi Umar ya jaddada cewa tallafin ba diyya ba ne, illa wani taimako ne da gwamnati ta bayar domin taimaka wa ’yan kasuwar su farfaɗo da sana'o'insu.
Ya kuma buƙaci waɗanda suka amfana da su ci gaba da addu'a ga Allah Maɗaukakin Sarki domin hana sake faruwar irin wannan bala'i.

Source: Facebook
’Yan kasuwa sun gode wa gwamnan
Wasu daga cikin ’yan kasuwar da suka amfana da tallafin sun bayyana godiyarsu ga Gwamna Ahmed Aliyu bisa matakin da ya ɗauka na taimaka musu.
Sun ce tallafin zai taimaka musu wajen sake fara kasuwancinsu da kuma farfaɗo da hanyoyin samun kuɗin shiga.
Haka kuma, sun yi alƙawarin ci gaba da bai wa gwamnatin Aliyu goyon baya.
An kai karar gwamnatin Sokoto
A wani labarin, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, ya maka gwamnatin jihar a kotun ƙoli ta jihar kan zargin ƙin ba shi rahoton kwamitin binciken shari'a da ya binciki gwamnatinsa.
Tambuwal, wanda ya mulki jihar daga shekarar 2015 zuwa 2023, yana neman kotu ta tilasta wa gwamnatin jihar fitar da cikakken rahoton kwamitin.
An shigar da ƙarar mai lamba SS/133/2026 a gaban Mai Shari'a Mohammed Mohammed na Babbar Kotun Jihar Sokoto mai lamba shida, ta hannun lauyan Tambuwal, U.O. Sule (SAN).
Asali: Legit.ng
