Rigima Sabuwa: Tambuwal Ya Maka Gwamnatin Sokoto Kara gaban Kotu

Rigima Sabuwa: Tambuwal Ya Maka Gwamnatin Sokoto Kara gaban Kotu

  • Aminu Tambuwal ya shigar da ƙara a babbar kotun Sokoto, yana zargin gwamnatin jihar da ƙin ba shi rahoton binciken gwamnatinsa
  • Rahoton ya shafi binciken ayyuka da harkokin kuɗi na shekaru takwas da Tambuwal ya yi yana mulkin jihar daga 2015 zuwa 2023
  • Babbar kotun ta sanya ranar 9 ga Nuwamba, 2026, domin sauraron ƙarar da tsohon gwamnan ya shigar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Sokoto - Tsohon gwamnan Sokoto kuma Sanatan Sokoto ta Kudu, Aminu Tambuwal, ya kai gwamnatin jihar ƙara a babbar kotun jihar bisa zargin hana shi samun rahoton kwamitin binciken shari’a da ya binciki gwamnatinsa.

Tambuwal, wanda ya mulki jihar daga 2015 zuwa 2023, yana neman kotu ta tilasta wa gwamnati sakin cikakken rahoton kwamitin da gwamnatin Gwamna Ahmed Aliyu ta kafa domin binciken ayyukansa da harkokin kuɗi da sauran al’amuran gwamnatinsa na shekaru takwas.

Kara karanta wannan

EFCC: An sanar da kotu yadda aka rika cire kudin kananan hukumomi ana ba jami'an gwamnati

Tambuwal ya shigar da kara kan gwamnatin Sokoto
Sanata Aminu Waziri Tambuwal da Gwamna Ahmad Aliyu na jihar Sokoto Hoto: Aminu Waziri Tambuwal Media Office, Dr. Ahmad Aliyu Sokoto
Source: Facebook

An shigar da ƙarar a babbar kotun Sokoto

An shigar da ƙarar mai lamba SS/133/2026 a gaban Mai Shari’a Mohammed Mohammed na Babbar Kotun Jihar Sakkwato mai lamba shida, ta hannun lauyan Tambuwal, U.O. Sule, SAN, cewar rahoton jaridar The Punch.

Waɗanda aka shigar da ƙarar a kansu sun haɗa da Gwamna Ahmed Aliyu, Antoni-Janar kuma Kwamishinan Shari’a na jihar, da kuma Hukumar Bincike ta Jihar Sakkwato.

Kwamitin binciken, wanda tsohon Alkalin Alkalai na Jihar Gombe, Mai Shari’a Mu’azu Pindiga, ya jagoranta, ya gudanar da zaman sauraron bayanai kan ayyukan gwamnatin Tambuwal kafin ya miƙa rahotonsa ga gwamnatin jihar.

Tambuwal ya ce an hana shi samun rahoton

Sai dai Tambuwal ya yi zargin cewa gwamnati ta ƙi ba shi rahoton duk da cewa ya halarci zaman binciken kuma ya shiga cikin tsarin gudanar da shi.

A cikin takardar ƙarar da ya shigar, tsohon gwamnan ya nemi kotu ta umarci waɗanda ake ƙara su ba shi cikakken rahoton, yana mai cewa yana da haƙƙin sanin sakamakon binciken da shawarwarin da kwamitin ya gabatar.

Kara karanta wannan

Tirkashi: An huro wutar da za ta iya sanya INEC hana Pantami da wasu yin takara a 2027

Ya bayar da hujjar cewa, bayan ya amince a bincike shi kuma ya shiga cikin tsarin binciken, doka da ƙa’idar adalci sun ba shi damar sanin abin da binciken ya gano.

Yana neman damar kare kansa

Tambuwal ya kuma ce samun rahoton yana da muhimmanci domin ya samu damar mayar da martani ga duk wani sakamako ko zargi da ka iya shafar sa.

Tsohon gwamnan ya kuma nemi kotun ta yanke hukunci kan ko waɗanda ake ƙara za su iya hana shi samun rahoton bisa doka bayan kammala ayyukan kwamitin binciken.

Kotun za ta saurari ƙarar a watan Nuwamba

Shigar da ƙarar ta mayar da takaddamar da ake yi kan rahoton binciken gaban kotu, inda Tambuwal ke neman a yi amfani da ikon shari’a wajen warware abin da ya bayyana a matsayin ci gaba da hana shi samun takardar.

An sanya ranar 9 ga Nuwamba, 2026, domin sauraron ƙarar wadda tsohon gwamnan kuma jigo a jam'iyyar ADC ya shigar.

Tambuwal ya kai gwamnatin Sokoto kara
Sanata Aminu Waziri Tambuwal a zauren majalisar dattawa Hoto: Aminu Waziri Tambuwal
Source: Twitter

Tambuwal ya yi magana kan masu shiga ADC

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanata Aminu Waziri Tambuwal, ya bayyana irin 'yan siyasar da ke shiha jam'iyyar ADC.

Tambawul ya ce 'yan siyasar da ke da ƙarfin guiwa kuma suka himmatu wajen yi wa jama'a hidima maimakon neman amfanin kansu ne kaɗai za su iya shiga jam'iyyar ADC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng