Gobara
Hukumar kashe gobara ta jihar Kano, ta bayyana irin barnar da gobara ta yi a cikin watan Nuwamban 2024. Hukumar ta ce gobara ta lalata kayayyakin miliyoyin Naira
Mummunar gobara ta yi barna a jihohin Yobe, Kwara, da Taraba, inda ta kone shaguna da wuraren hutu tare da haddasa asarar dukiyoyi masu tarin daraja.
Wata gobara da ta tashi a ofishin hukumar zabe ta INEC a Delta, ta lalata kayayyaki. Lamarin ya auku ne a daya daga cikin ofisoshin hukumar na kananan hukumomin
wata gobara da ta kama sakamakon haɗuwar motar katifa da wayar wutar lantarki ta babbake kayan maƙudan kudi a wata kasuwa a Ilorin a jihar Kwara.
'Yan kasuwa sun gamu da jarrabawa a Yobe. An wayi gari da mummunan iftila'in gobara. Hukumar SEMA ta jihar ta sanar da Legit adadin asarar da aka tafka.
An samu tashin gobara a cikin daren ranar Lahadi a babban birnin tarayya Abuja. Gobarar dai ta tashi a kasuwar da ke cikin rukunin gidajen Trademore.
An samu tashin gobara a wata fitacciyar kasuwa da ke jihar Legas. Gobarar wacce ta tashi ta lalata shaguna masu yawa. Hukumomi sun ce ba a samu asarar rai ba.
An samu tashin gobara a harabar ofishin gidan rediyon Najeriya da ke Legas. Jami'ai sun yi kokarin kashe gobarar wacce ba a san musababbin tashin ta ba.
An samu tashin gobara a asibitin koyarwa na jam'iar LAUYECH da ke jihar Oyo. Gobarar wacce ta tashi a asibitin ta jawo asarar dukiya ta miliyoyin naira.
Gobara
Samu kari