An Rage Mugun Iri a Katsina, Fitsararren Ɗan Bindiga da Ya Addabi Mutane Ya Mutu

An Rage Mugun Iri a Katsina, Fitsararren Ɗan Bindiga da Ya Addabi Mutane Ya Mutu

  • Jami'an tsaro sun yi nasarar kawo ƙarshen daya daga cikin harsabiban yan bindiga a jihar Katsina da ke Arewa maso Yamma
  • An kashe wani fitaccen dan bindigan ne yayin arangama tsakanin sojoji, ’yan sanda da jami’an C-Watch a Katsina
  • Rahotanni sun ce marigayin na da alaƙa da ƙungiyar Kachalla Maha, kuma ana zarginsa da addabar mazauna Matazu da makwabtansu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Katsina - Rahotanni sun bayyana cewa an kashe wani da ake zargi da jagorantar ’yan bindiga a jihar Katsina.

Majiyoyi sun tabbatar da kisan harsabibin dan bindigan mai suna Wakiyu, yayin arangama tsakanin jami’an tsaro a Katsina.

An kashe hatsabibin dan bindiga a Katsina
Taswirar jihar Katsina da aka hallaka dan bindiga. Hoto: Legit.
Source: Original

Shafin Bakatsine da ke kawo rahotanni game da rashin tsaro musamman a Arewacin Najeriya shi ya bayyana haka a X.

Yadda aka kashe hatsabibin dan bindiga

Kara karanta wannan

'Yan bindiga na barazanar kashe mata da mijin da suka sace, Atiku ya yi magana

Majiyar ta yi zargin cewa Wakiyu na da alaƙa da ƙungiyar fitaccen shugaban ’yan bindiga, Kachalla Maha.

Maha ya daɗe yana addabar mazauna yankin Matazu da ke Katsina da yankunan da ke kewaye.

An kashe Wakiyu ne a garin Damari sa ke ƙaramar hukumar Sabuwa a jihar Katsina,

An yaba wa dakarun Birged ta 17 da ke Katsina bisa ci gaba da gudanar da ayyukan yaƙi da ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai a faɗin jihar.

Rahoton kashe-kashen ya zo ne a daidai lokacin da jami’an tsaro ke ci gaba da gudanar da ayyuka a wasu sassan Arewa maso Yammacin Najeriya, inda ’yan bindiga ke kai hare-hare kan al’umma, sace mutane tare da kawo cikas ga noma da sauran harkokin tattalin arziki.

A cikin saƙon da aka wallafa, sanarwar ta ce:

“Labari mai daɗi: An kashe fitaccen ɗan bindiga Wakiyu a jihar Katsina.
“An kashe Wakiyu, wanda ake zargin yana da alaƙa da ƙungiyar Kachalla Maha, yayin arangama tsakanin sojoji, ’yan sanda da jami’an C-Watch a Damari, ƙaramar hukumar Sabuwa ta jihar Katsina. Ana zarginsa da addabar mazauna Matazu da yankunan da ke kewaye.

Kara karanta wannan

Tinubu Must Go: Yan sanda sun faɗi abin da ya faru bayan zargin hana masu gangami

“Ina yaba wa dakarun Birged ta 17 da ke Katsina bisa ci gaba da kai farmaki kan ’yan bindiga a faɗin jihar. Waɗannan ayyuka suna da muhimmanci wajen yaƙi da rashin tsaro da kuma dawo da zaman lafiya a yankunan da abin ya shafa.
“Allah Ya ci gaba da ba jami’an tsaronmu nasara tare da kawo wa mazauna jihar Katsina sauƙi mai ɗorewa.”

Karin bayani na tafe.....

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.