Seyi Tinubu da Kansa Ya Tabbatar da Halin Kunci, Ya Nemi Alfarmar Yan Kasa

Seyi Tinubu da Kansa Ya Tabbatar da Halin Kunci, Ya Nemi Alfarmar Yan Kasa

  • Seyi Tinubu ya amince cewa sauye-sauyen tattalin arzikin gwamnati sun jefa iyalai cikin wahala a Najeriya
  • Ya bayyana cire tallafin man fetur, sauye-sauyen kuɗin musaya da tsarin haraji a matsayin matakan da za su samar da damarmaki
  • Seyi ya ce zuba jari a hanyoyi, wutar lantarki, noma da masana’antu zai bunƙasa tattalin arziki, samar da ayyukan yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Seyi Tinubu, ɗan Shugaba Bola Tinubu, ya buƙaci ’yan Najeriya su amince da sauye-sauyen tattalin arzikin gwamnatin tarayya.

Seyi ya ce an tsara su ne domin samar da damarmaki da kyakkyawar makoma ga matasa masu tasowa.

Seyi Tinubu ya roki yan Najeriya
Dan shugaban kasa, Seyi Tinubu da mahaifinsa, Seyi Tinubu. Hoto: Seyi Tinubu, Dada Olusegun.
Source: Instagram

Ya bayyana hakan ne a taron farko na Seyi Tinubu Colloquium, mai taken “Makoma Daya Muke Ginawa Tare,” wanda aka gudanar a otal din Eko, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Bankin Duniya ya zuga Tinubu kan halin da ƙasa ke ciki, ya yi alƙawari

Kokarin da Bola Tinubu ya yi a Najeriya

A jawabin maraba da ya gabatar, Seyi, wanda zai yi bikin zagayowar ranar haihuwarsa ranar 13 ga Oktoba, ya ce kowace tsara tana gadon ƙasar da ba ita ta zaba ba, amma tana da alhakin tsara makomar waɗanda za su zo bayanta.

Ya ce gwamnatin Shugaba Tinubu ta zaɓi fuskantar ƙalubalen Najeriya domin amfanin al’ummomin da za su zo nan gaba.

Ya ce:

“Shugaba Bola Ahmed Tinubu bai zaɓi Najeriya ba, haka kuma bai zaɓi irin Najeriya da ya gada daga magabatansa ba. Duk da haka, gwamnatinsa ta zaɓi fuskantar ƙalubalen ƙasar nan, ba don amfaninta kaɗai ba, har ma domin waɗanda za su zo bayanta, wato mu matasa.”

Seyi ya bayyana cire tallafin man fetur, gyaran tsarin musayar kuɗaɗen waje da sauye-sauyen tsarin haraji a matsayin manyan matakan da ke shafar alkiblar tattalin arzikin ƙasar.

Seyi Tinubu ya tabbatar ana wahala a Najeriya
Dan shugaban kasa, Seyi Tinubu. Hoto: Seyi Tinubu.
Source: Twitter

Seyi ya tabbatar da ana cikin kunci

Kara karanta wannan

Tinubu Must Go: Yan sanda sun faɗi abin da ya faru bayan zargin hana masu gangami

Da yake amincewa da wahalhalun da sauye-sauyen suka jawo, ya ce tasirinsu ya fi shafar iyalan da matsin tattalin arziki ya takura wa kasafin kuɗinsu.

Ya ce:

“Cire tallafin man fetur, gyaran tsarin musayar kuɗaɗen waje da sake fasalin haraji, duk matakai ne da suka shafi yadda Najeriya ke samun kuɗi, kashe su da kuma samar da damarmaki.
“Sauye-sauyen ba su kasance masu sauƙi ba. Iyalai sun shiga matsin lamba saboda ƙarancin kuɗi, kuma zafin matsalar ya bayyana nan take, yayin da yake da wuya a ji ko a ga amfanin da za a samu nan gaba. Duk da haka, amfanin yana nan.”

Ya kuma jaddada muhimmancin ƙarfafa cibiyoyin da ke faɗaɗa damar samun ilimi da rance, yana mai cewa hakan zai taimaka wa ’yan Najeriya wajen yin gogayya a kasuwannin duniya.

Seyi ya ce yana goyon bayan shirin sauye-sauyen shugaban ƙasa ne saboda matasan Najeriya suna buƙatar tattalin arzikin da mutum zai iya samun sakamako mai kyau sakamakon ƙoƙarinsa.

Ya ce:

“Ina goyon bayan sauye-sauyen Shugaba Bola Ahmed Tinubu saboda mu ne za mu gaji makomar da shugabannin yau suke ginawa.”

Kara karanta wannan

Atiku ya magantu kan tsadar kayan noma, ya fadi mafita tare da sukar Tinubu

Seyi Tinubu ya ki gaisawa da Bashir

Mun ba ku labarin cewa tsohon hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad, ya yi martani kan bidiyon da ke nuna Seyi Tinubu ya tsallake shi yayin gaisawa da mutane.

Bashir Ahmad ya bayyana cewa sun raka Seyi Tinubu ne domin ganawa da kungiyar mata, ba wai domin ganawa da shi kai tsaye ba.

Bidiyon ya jawo ce-ce-ku-ce a Najeriya, inda mutane da dama ke yi wa Bashir ba'a saboda yadda yake tallata APC da Bola Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.