Fasto Ya Gano Atiku na da Sa'a a 2027, Ya Ce Tinubu zai iya Faduwa Warwas
- Shugaban cocin ta INRI, Primate Elijah Ayodele, ya bayyana hanyoyi uku da zaben shugaban kasa na 2027 zai iya dauka, tare da gargadin cewa Shugaba Bola Tinubu ka iya faduwa
- Faston din ya kuma yi kashedin cewa zaɓen na iya haifar da dokar ta ɓaci, tare da kiran Shugaba Tinubu da iyalansa da su maida hankali kan addu'a ba kama kafar yaro
- Ayodele ya kuma nuna cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar yana da damar yin nasara amma matakan da yake ɗauka ka iya gurgunta damarsa ta kai wa ga ci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Lagos – Shugaban Cocin INRI da ke Oke-Afa a jihar Lagos, Primate Elijah Ayodele, ya fito fili ya bayyana hasashensa game da abubuwan da za su iya faruwa a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.
Hakan na zuwa ne bayan manyan APC, ciki har da Sanata Abdulaziz Yari suna nuna cewa shugaban kasa Bola Tinubu zai yi nasara a 2027.

Source: Facebook
Leadership ta rahoto cewa Ayodele ya bayyana hakan ne a cikin wani bidiyo da ya yaɗu a kafafen sada zumunta a ranar Lahadi, inda ya bayyana cewa Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ma ka iya fuskantar barazana.
Abubuwa 3 da za su faru a 2027
Yayin da yake bayani game da zaben 2027, Primate Ayodele ya bayyana cewa:
"Ina son in faɗawa Tinubu gaskiya kai tsaye. Idan aka je zabe karo na biyu, tsakani da Allah ba za ka ci nasara ba.
"Abubuwa uku za su iya faruwa da wannan zaɓen: Zaɓen zai iya tafiya zuwa zaɓen zagaye na biyu wanda zai iya ƙayar da Tinubu; ko kuma zaɓen ya haifar da dokar ta ɓaci ta hanyar da ake son dakatar da shi gaba ɗaya ba tare da sakamako ba; sannan na uku, Tinubu yana buƙatar addu'a sosai."
Ya ƙara da cewa idan har Shugaba Tinubu ya ƙarfafa kansa don neman tazarce na aiki karo na biyu, za a iya fuskantar asarar rayuka ko rashin kwanciyar hankali wanda ke buƙatar takatsantsan.
Bayanin Elijiah Ayodele kan Atiku Abubakar
Game da tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, faston ya bayyana cewa Atiku yana da ɗan sa'a a yanzu yayin da mutane ke son ƙaurace wa sake zaɓen Tinubu, amma kuskure a matakan siyasarsa na na iya zama sanadiyyar faɗuwarsa.
"Tokala ko ƙa'idodin siyasa za su iya kashe damar Atiku. Atiku shi ne zai gurgunta kansa. Idan ba su kula ba, Tinubu zai iya sake kayar da shi duk da rashin goyon bayan da yake fuskanta a yanzu,"
Inji Primate Ayodele.

Source: Facebook
Ga bidiyon da Ayodele ya yi magana da da shafin DGov ya wallafa a X:
Bayanin INEC kan 'yan takara
A wani labarin, mun ruwaito cewa INEC ta watsar da wani rahoton ƙarya da ke yaɗuwa a intanet wanda ake daƙawar cewa sanarwa ce ta musamman kan 'yan takarar gwamna a jihohi shida.
Hukumar ta ayyana cewa jihohin da abin ya shafa sun haɗa da Zamfara, Gombe, Delta, Plateau, Yobe da kuma Kano, inda ta tabbatar da cewa wannan labari na ƙarya ne kuma bai fito daga gare ta ba.
A cikin wata sanarwa da ta wallafa, INEC ta buƙaci al'umma da su yi watsi da wannan rahoton sannan su maida hankali kadai kan bayanan da ta fitar ta hanyoyin sadarwarta na hukuma.
Asali: Legit.ng

